Hukumar Kula da Jami’o’in Kasa (NUC) ta kaddamar da yunkurin gabatar da harsunan Tib da Nupe a matsayin manhajojin karatu a jami’o’in Nijeriya.
Wannan yunkuri, da Sakataren Zartarwa na NUC, Farfesa Abdullahi Ribadu, ke jagoranta, na nufin sanya wadannan harsuna a matsayin darussa na digirin farko, wanda zai zama babban mataki wajen amincewa da kuma adana gadon harsunan Nijeriya.
- NDLEA Ta Cafke Mutane 230 Da Miyagun Ƙwayoyi A Kano
- Akwai Bukatar Karfafa Hadaka Domin Ciyar Da Tashoshin Jiragen Ruwa Gaba A Afirka —Dantsoho
A matsayin wani bangare na wannan tsari, an dauki kwararru daga jami’o’in Nijeriya domin tsara Ka’idojin Mafi Karancin Darussan Asali (CCMAS) don sabbin shirye-shiryen.
Wannan mataki ya sanya harsunan Tib da Nupe a matsayin sabbin kari a cikin jerin harsunan da ake koyarwa a jami’o’in Nijeriya.
A da ana koyon wadannan harsuna ne a matsayin darussa na zabi ko batutuwan bincike, amma yanzu za a samar da cikakkun shirye-shiryen digiri da aka tsara domin samar da dalibai masu ilimi mai zurfi a fannin harshe, adabi, da al’adun zamantakewa.
Shirye-shiryen kuma suna da nufin karfafa adana al’adu da kuma yaki da barazanar bacewar harsuna.
A cewar bayanan NUC, manyan masu ba da shawarwari don shirye-shiryen su ne Farfesoshi Mary Adebayo (Tib) da Rebecca K. D. (Nupe).
Masu tallafawa ci gaban darussan sun hada da Farfesoshi Muhammad Alkali da Musa Bawa don Tib, da Farfesoshi John Akosu Adeiyongo da Nguton Sambe don Nupe.
Kwamitin kuma ya hada da wakilan NUC: Florence Onuoha, Chinenye Augustine, Kate Omotayo Onaiyekan, da Hadiza Kalla.
Idan za a iya tunawa an gudanar da wani taron bita na kwanaki hudu a Hedikwatar NUC daga 21 zuwa 24 ga Oktoba, 2025, inda aka hada kwararrun masu ruwa da tsaki don shirya tsarin CCMAS.
Wannan yunkuri ya biyo bayan damuwa kan rauni da kuma barazanar da harsunan gida fiye da 500 na Nijeriya ke fuskanta, da dama daga cikinsu suna karkashin inuwa ta harshen Turanci da manyan harsunan gida kamar Hausa, Yoruba, da Igbo.
Harsunan Tib, da ake magana da shi sosai a Jihar Benue da kewaye, da Nupe, wanda ya yi fice a jihohin Niger, Kogi, da Kwara, yanzu za su samu dandamali na ilimi da aka tsara, wanda zai shirya dalibai don koyarwa, bincike, da habaka wadannan harsuna a makarantu, kafofin yada labarai, da cibiyoyin al’adu.














