Gwamnatin Tarayya Ta Ware Naira Biliyan 336 A Kasafin Kuɗin Bana Don Manyan Ayyuka

Daga Sabo Ahmad.

Gwamnatin tarayya ta ware zunzurutun kuɗi naiara biliyan 336, daga cikin kasafin kuɗin bana, ga ma’aikatu da sassan gwamnati da kuma hukumomi, don gudanar da manyan ayyuka, a farkon watanni uku na shekarar bana.

“Yanzu haka ana ƙoƙarin samar da cikon  naira biliyan 14, don fara bai wa hukumomin da ayyukansu suka fi muhimmanci,” Mataimakiyar  Daraktan ma’aikatar kuɗi, Patricia Deworitshe,  ta bayyana haka, a wani jawabi da ta yi a jiya.

Ta ce, sashen kula da wutar lantarki, da ayyuka da gidaje, su ne suka fi samun kaso ma fi tsoka na naira biliyan 90, sai ma’aikatar tsaro wadda ke da naira biliyan 71, sai sufiri mai naira biliyan 30. Daga nan sai noma da aka ware masa naira biliyan 30, da kuma albarkataun ruwa mai naira biliyan 12. Saura sassan kuwa dukkansu an ware musu naira biliyan 103, kamar yadda aka faɗa a cikin bayanin.

Ministan kuɗi, Mista Kemi Adeosun, ya bayyana cewa,an fifita kasafin kuɗin na bana ne a kan farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasa, da kuma sababbin tsare-tsaren da za su taimaka wajen bunƙasa ƙasar.

Ya ce, a kasafin kuɗin, gwamnatin tarayya za ta fi bayar da ƙarfi a kan manyan ayyuka waɗanda za su bunƙasa tattalin arziƙin ƙasa domin samar da guraben ayyuka ga ‘yan ƙasa.

“Duk da matsin tattalin arziƙin da aka yi fama da shi, gwamnatin tarayya, ta iya samar da kuɗaɗen da za a  gudanar da wasu manyan ayyuka, wanda hakan ke nuna ƙoƙarin gwamnatin na bunƙasa tattalin arziƙin ƙasar nan,” kamar yadda ministan ya faɗa.

Exit mobile version