Gwamnatin Tarayya ta miƙa ta’aziyyar ta ga iyalan waɗanda suka rasa ran su a haɗarin jirgin ruwa da ya faru kwanan nan a yankin Borgu na Jihar Neja, wanda ya yi sanadin mutuwar kimanin mutum 32.
A wata sanarwa da ya fitar a yau, Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana wannan lamari a matsayin abin da “ya tayar da hankali.”
- ‘Yan Nijeriya Suna Shan Wahala A Lokacin Da Gwamnatin Tinubu Ta Fi Damuwa Da Aljihunta – Sule Lamido
- 2027: Idan Kana Son Tarwatsa PDP, To Ka Dawo Da Peter Obi – Wike
Ya ce: “Wannan ibtila’i ya yi matuƙar tayar da hankali, kasancewar ya faru ne cikin ƙasa da watanni huɗu bayan ambaliyar ruwa mai muni da ta afku a Mokwa, shi ma a Jihar Neja.
“Muna miƙa ta’aziyyar mu ta musamman ga iyalan waɗanda abin ya shafa, gwamnatin jihar da kuma al’ummar Neja. Jimamin mu da addu’o’in mu suna tare da duk wanda wannan ibtila’i ya shafa.”
Ministan ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta umurci Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) da ta samar da dukkan tallafi da ake buƙata ga iyalan waɗanda suka mutu da waɗanda suka tsira, tare da yin aiki kafaɗa da kafaɗa da gwamnatin Jihar Neja domin tabbatar da gaggawar tallafi da taimako.
Haka kuma, gwamnatin ta umurci Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta Ƙasa (NOA) da ta gudanar da babban kamfen na wayar da kai a faɗin ƙasar nan domin ƙara faɗakar da jama’a kan matakan tsaro yayin amfani da hanyoyin ruwa.
Idris ya yaba wa gwamnatin Jihar Neja, ta hannun Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Jiha, bisa gaggawar gudanar da aikin ceto da ya tabbatar an tantance dukkan fasinjojin da ke cikin jirgin da ya yi hatsarin.
Ya ce: “Zan yi amfani da wannan dama in sake tunatar da jama’a da su riƙa bai wa batun tsaro muhimmanci yayin tafiya ta hanyoyin ruwa.
“Musamman, babu wanda ya kamata ya shiga tafiyar jirgin ruwa ba tare da sanya rigar kariya ta musamman ba. Matakan tsaro na iya ceton rayuka.”
Ya yi addu’ar samun rahamar Allah ga rayukan waɗanda suka salwanta tare da yi wa waɗanda suka tsira fatar samun lafiya cikin gaggawa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp