Ministan ma’adanai, Dele Alake, ya yaba wa tawagar masu zuba jari daga kasar Medico a shirinsu na shigowa tarayyar Nijeriya don zuba jari a bangaren bunkasa ma’adanai.
Bayanin haka na cikin takardar sanarwar da jami’in watsa labarai na ministan, Segun Tomori ya Sanya wa hannun a ka kuma raba wa manema labarai a Abuja ranar Lahadi, ya kuma kara da cewa, Ministan ya ce, shugaban kasa Bola Tinubu ya yi tanadin abubuwan da zai saukka wa masu zuba jari a bangaren hakar ma’adanai hanyoyin yin harkokinsu ba tare da fuskantar matsala ba.
- Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Game Da Dabarun Warware Rikicin Isra’ila Da Falasdinawa
- Gwamnatin Kaduna Ta Kaddamar Da Kwamitin Mutum 8 Don Inganta Harkokin Aikin Hajjin 2024
Abubuwna sun hada janye haraji a kan kayan aikin hakar ma’adanai da za su shigo da su da kuma saukaka zirga-zirgar ma’adanan da aka haka zuwa kasashen su.
Ministan ya kuma ce, ana sa ran masu zuba jari a harkar ma’adanai a Nijeriya su sanya hannu a kan wata yarjejeniyar bunkasa wuraren da suke hakar ma’adanai don al’ummar yankuna suma su amfana da ayyuykan da ake yi a yankunansu.
Da yake gabatar da masu zuba jarin, jakadan kasa Medico mai barin gado, Adejare Bello, ya tabbatar wa da Ministan cewa, ofishin jakadancin Nijeriya ya tantance masu zuba jarin an kuma tabbatar da cewa, ‘yan kasuwa ne da suka himmatu da gudanar da sahihin kasuwanci wanda zai taimaka wajen bunkasa tattaliin arzikin Nijeriya.
Ambasada Bello ya bayyana cewa, ofishin jakadancin Nijeriya ya yi kusan shekara biyu yana tattauanwa da ‘yan kasuwar, ya kuma gabatar da su a gaban Ministan ne bayan an tabbtar da fatimtar juna a tsakaninsu.