Daga Sulaiman Ibrahim,
Majalisar zartaswa ta tarayya ta amince da kwangiloli na N64,686,536,230 na gina tituna da gadoji a sassa daban-daban na kasar nan, ciki har da babban birnin tarayya (FCT).
Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai da hulda da jama’a Garba Shehu da kuma ministan babban birnin tarayya, Malam Mohammed Musa Bello ne suka bayyana haka a yau Laraba yayin da suke zantawa da manema labarai na fadar shugaban kasa bayan kammala taron majalisar ministocin tarayya a fadar shugaban kasa. Villa, Abuja.
Shehu wanda ya bayyana hakan a madadin Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola, ya ce FEC ta amince da ayyuka 15, hanyoyi da gadoji kamar yadda ma’aikatar ta bukata.
Ya ce: “Na daya shi ne kwangilar gina kashi na biyu na aikin titi daga Ikot-Ekpene-Aba zuwa Owerri akan kudi N40,157,000,000. Za a kammala aikin a cikin watanni 30.
“Wani aikin da ya samu amincewar shi shine gina titin Offa Bypass kashi na biyu a karamar hukumar Offa ta jihar Kwara. Shima akan N4,335,000,000 ne, wanda za a kammala shi nan da watanni 12.
“Wani kuma shi ne kiyasin da aka yi wa kwaskwarima na gyaran hanyar Alesi-Ugep a jihar Cross River. Kudin farko dai ya kai Naira biliyan 11.221, wanda yanzu ya kai Naira 14.74, tare da karin watanni shida akan adadin kwanakan farko.
“Sauran hanyoyin guda goma sha daya za a yi su ne a yankuna daban-daban a fadin kasar.”