Daga Bello Hamza,
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, babu mutumci kuma abun ki ne wani Malamin addini ya yi amfani da lokacin bikin Kirsitimeti, lokacin da ake kokarin wanzar da zaman lafiya, yana yada tare da ruruta wutar kiyayya da rarrabuwa a tsakanin al’umma Nijeriya.
A sanarwa da Ministan Yada Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed, ya raba wa manema labarai a Legas ya bayyana haka, ya ce, shiga irin wannan taragon ga Malaman addini yana iya haifar da matsalar da ba a san iyakan inda za ta kai ba.
Maitaimaki na musamman ga Ministan, Mr Segun Adeyemi, ya sanya wa sanarwa hannu, Ministan ya kuma kara da cewa, duk kuwa da cewa, Malaman addini na da hakkin sanar da masu mulki gaskiya amma bai kamata su lullube gaskiyar da suke son fada ba a cikin fushi da kiyayya da kokarin rarraba kan al’umma da kuma haifar da rarrabuwa ta bangaren addini.
Ministan ya kuma ce, kira da a canza gwamnati ba ta hanyar jefa kuria ba wani bu ne da ya yi kama da kira ga tashin hankali da rudani a kasa.
Ya kuma ce, duk matsalolin da Nijeriya ke fuskanta a halin yanzu wani abu ne da za a iya maganinsa musamman in dukkan shugabanin daga bangarori suka hada hannun aka kuma yi aiki tare.
Ya ce, ba za a iya maganin matsalolin ba in har wasu suka koma gefe suna zagi tare da ganin laifin wasu.”
A sakonsa na kirismeiti ne Bishop na cocin katolika na yankin Sakkwato, Reb. Matthew Kukah, ya bayyana cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari na jagorantar kasa ce wadda ta gama rushewa.
Ya kuma kara da cewa, in har da wani ne ba Musulmi ba ya ke jagorantar kasar nan a halin yanzu da tuni an yi msa juyin mulki. “Da tuni an samu juyin mulki ko kuma yaki ya barke a kasar, inji shi.”