Gwamnatin Amurka, a ƙarƙashin shugabancin Donald Trump, ta bayyana shirin rufe ofisoshin jakadanci a wasu ƙasashen Afrika, ciki har da Eritrea, Gambiya, Sudan ta Kudu, Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo, Lesotho, da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.
Wannan mataki na zuwa ne a matsayin wani ɓangare na sauyin tsarin diplomasiya da ci-gaba da Amurka take yi a yankin, wanda hakan na jawo damuwa game da makomar ci gaban tattalin arziƙi, da ilimi, da kiwon lafiya a Afrika.
- Trump Ya Dakatar da Harajin Da Sanya Wa Ƙasashen Duniya, Ya Ƙi Cire Wa China
- Guguwar Kudin Fito Na Gwamnatin Trump: Dabara Ko Hauka?
A wannan sabon shirin, Amurka ta rage ayyukan ma’aikatar harkokin wajenta a yankin, musamman a fannin kula da dimokuraɗiyya, haƙƙin ɗan adam, da batutuwan sauyin yanayi.
Har ila yau, Amurka ta mayar da hankali kan wasu “ƙasashe masu muhimmanci,” wanda hakan ya haifar da ƙarancin tallafi ga ƙasashen da ba su cikin wannan jerin, ciki har da ƙasashen kamar Equatorial Guinea, Eritrea, da Gabon. Wannan ragin tallafi ya shafi shirye-shiryen rigakafin zazzaɓin cizon sauro, da taimakon noma, da kiwon lafiya.
A cikin wannan yanayi, ƙasashen Afrika na ƙoƙarin nemo hanyoyin magance wannan giɓin tallafi, inda Nijeriya ta ware dala miliyan 200 don taimakawa ci gaban kiwon lafiya a cikin ƙasar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp