Gwamnatin Yobe Ta Tura Dalibai 1,400 Karatu Waje –Gwamna Gaidam

Daga Muhammad Sani Chinade, Damaturu

Gwamnan jihar Yobe, Alhaji Ibrahim Gaidam, ya bayyana cewar, gwamnatin jihar a yanzu haka ta tura kimanin daliban jihar 1,400 ya zuwa manyan makaratun karo ilimi a wasu kasashen ketare.

Gwamnan ya bayyana hakan ne ya yin da ya ke karbar bakuncin mataimakin shugaban jami’ar kula da kiwon lafiya, kimiyya da fasaha ta Al-Madain Abdullah Hassan El-Bashir da ke kasar Sudan, da ya kawo ziyara a gidan gwamnatin Jihar dake garin Damaturu.

Ya kara da cewar Jihar Yobe za ta hada gwiwa da Jami’ar Al-Madain, don ganin cewar daliban jihar da yawa sun amfana musamman kan bangaren samun horo na aikin likitanci, da sanin magunguna da horo a kan darasin injiniya, da zaiyana da makamantansu.

Kamar yadda gwamnan ya ce a yanzu haka gwamnatin Jihar Yobe ta dauki dawainiyar daliban Jihar kusan kimanin 1400 ya zuwa kasashen ketare don karo ilimi, ciki har da kasar Sudan cikinsu har da dalibai mata kimanin 80 da ke karatu a Jami’ar Ahfad.  Tun farko da ya ke jawabi Dr. El-Bashir, wadda tsohon Janar ne na rundunar sojan kasar Sudan ne, ya ce jami’arsu ta Al-Madain, a shirye ta ke da ta ba da dama ga daliban Jihar Yobe don samun ilimi mai inganci kamar yadda ake bukata, don mayar da Jihar Yobe wacce ke da likitoci masun yawan gaske a fadin kasar nan.

Ya kara da cewa, dangantakar da ke tsakanin Nijeriya da kasarmu ta Sudan dangantaka ce mai matukar armashi tsawon lokaci musamman kan abin da ya shafi tattalin arziki, da siyasa, da al’adu da ilimi da   sauransu.

Exit mobile version