Gwamnan Jihar Yobe Mai Mala Buni, ya amince da bai wa Malaman makaranta akalla 4,000 bashin Naira miliyan 500 domin bunkasa harkokin noma a fadin jihar.
Gwamnan ya sanar da hakan a sanarwar manema labaru, mai dauke da sa-hannun Darakta Janar kan hulda da yan jaridu da kafafen yada labaru, Alhaji Mamman Mohammed, inda ya kara da cewa, za a bayar da bashin kan hanyoyi biyu; domin inganta jindadin malaman tare da daura damarar shiga daminar wannan shekara ta 2023.
Alhaji Mamman ya kara da cewa, kowane daya daga cikin wannan adadi na malamai 4,000 zai karfi kimanin naira 120,000 wajen shiga harkar noman don bunkasa jihar da abinci.
Bugu da kari kuma, Gwamna Buni ya shawarci wadanda za su ci gajiyar kudin su yi amfani da tallafin ta hanyar da ya dace, kuma bisa manufar da aka basu bashin.
Sanarwar ta kara da bayyana cewa, bashin zai gudana ne a karkashin bankin ‘Yobe Microfinance’ tare da biyan sa cikin watanni 24 (shekara biyu) ta hanyar Ma’aikatar kudi da Ma’aikatar Kananan hukumomi da harkokin masarautu na jihar Yobe.
A nashi bangaren, Manajan Darakta a Bankin Yobe Microfinance, Dr. Sheriff Al-Muhajir, ya bayyana cewa shirye-shiryen aiwatar da raba kudin ya kankama a matakin karshe, wanda kuma nan da lokaci kadan za a fara raba kudin kafin shigar damina.
“Yanzu haka muna aiki a matakin karshe na shirye-shiryen aiwatar da bayar da bashin.”
“Sannan zan kara da sanar da cewa, makasudin Mai Girma Gwamna Mai Mala Buni kan wannan shirin, shi ne wadanda zasu ci gajiyar wannan bashin, za su yi amfani da bashin wajen yin noma domin bunkasa samar da abinci.” In ji Al-Muhajir.