Gwamnonin Jihohi 36 na Tarayyar Nijeriya za su gana da dukkan hukumomin tattalin arziki da kudade na kasar nan, da nufin kawar da matsalolin da suka dabaibaye tsaron jihohinsu, wajen samar da ingantacciyar hanyar sarrafa kudade.
Taron wanda zai gudana a ranar Talata 4 ga watan Afrilu, bisa ga gayyatar da Darakta-Janar na kungiyar gwamnonin Nijeriya, Mista Asishana Bayo Okauru, ya bayar, domin tabbatar da halartar dukkan masu ruwa da tsaki cikin lamarin.
A cewar sanarwar da daraktan yada labaran kungiyar, Abdularaque Bello Barkindo, ya ce wadanda aka gayyata zuwa taron sun hada da EFCC, ICPC, Hukumar Kula da Harajin Cikin Gida ta Tarayya (FIRS) da Babban Bankin Nijeriya (CBN).
Bugu da kari, ya ce taron zai kuma yi la’akari da zurfafa gudanarwa da fadada manufofin rashin kudi wanda ya fara aiki tun daga lokacin da aka sauya fasalin kudin kasar nan, a shekarar da ta gabata.
Ya ce, “Wannan taro an shirya shi ne don nemo mafita kan matsalolin kudi.
“An shawarci dukkan gwamnoni da su bai wa taron fifiko don tattauna abubuwan da ke da nasaba da shi,” in ji shi.