Gwamnonin arewa maso yammacin Nijeriya sun garzaya Abidjan, domin halartar taron zamanantar da ayyukan gona da yadda ake sarrafawa ta hanyar masana’antu.
Gwamnonin su bakwai sun bar Nijeriya ne a ranar Laraba, 15 ga Nuwamba, wanda aka shirya za su gana da shugaban bankin raya Nahiyar Afirka, Dakta Akinwumi Adesina.
- Kasashen Afirka Na Cin Gajiyar Aikin Zamanintar Da Aikin Gona Na Sin
- Shugaban Kasar Sin Ya Gabatar Da Rubutaccen Jawabi Ga Taron Jagororin Masana’antu Da Kasuwanci Na APEC
A cikin sanarwar da mai magana da yawan gwamnan Jihar Zamfana, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ya ce sun tafi Abidjan ne domin amfani da damar wajen duba shirin zamanantar da ayyukan noma.
Ya kara da cewa gwamnonin guda bakwai sun hada da na jihohin Zamfara, Sakkwato, Jigawa, Kaduna, Katsina, Kano da kuma Kebbi.
“Gwamnonin yankin arewa maso yammacin Nijeriya za su gana da shugaban bankin bankasa nahiyar Afirka, Dakta Akinwumi Adesina da kuma tawagarsa.
“An shirya gudanar da taron ne a ranar 16 ga Nuwambar 2023, kuma zai hada da gabatar da bayanai kan zamanantar da ayyukan aikin gona.
“Shirin ya hada har da samar da masana’antu na musamman na noma ta yadda za a samu nasarar samar da wadataccen abinci, samar da ayyukan yi, bunkasa tattalin arziki ta hanyar sarraba amfanin gona a yankuna daban-daban.
“Mataimakiyar shugaban ayyukan noma na bankin bunkasa yankin Afirka, Dakta Beth Dunford za ta jagoranci gwamnoni kan yadda ake sarrafa amfanin gona ta hanyar masana’antu da kuma abubuwan da ya kamata gwamnonin su yi domin cin gajiyar shirin.
“Babban mashawarcin shugaban bankin raya Afirka kan masana’antu, Farfesa Oyebanji Oyelaran-Oyeyinka zai yi wa gwamnonin bayani kan irin mataki na daya da na biyu na shirin domin inganta shi a jihohinsu,” in ji Idris.