A daidai lokacin da kotunan sauraren korafe-korafen zaben gwamnoni a fadin tarayyar kasar nan ke shirin yannke hukunci, al’umma sun zura ido don ganin yadda za ta kasannce a wasu jihohin da ake ganin gwamnonin da ke kan karaga sun fi hawa kan tsini.
A jihohin fadin tarayyar kasar nan ana sa ran alkalan kotunan za su yanke hukuncin shari’o’in da ke gaban su a mako mai zuwa.
Tarihin yadda kotuna zaben gamnononi suke kasancewa a Nijeriya yana nuna cewa akalla za a iya soke zabe gwamna daya ko biyu a cikin shari’un da ake saurara a fadin tarayyar kasar nan.
A cikin kusan dukkan zabukan da aka yi tun daga shekarar 2003, akalla kotun daukaka kara ta cire gwamna daya inda dama a nan ne mataki na shari’a na karshe a kan shari’un gwamnoni daga shekarar 2011 da kuma kotun koli inda a nan ne take turnukewa a halin yanzu.
Bayan murnar cin zaben gwamna na shekarar 2019 a watan Mayu na shekarar 2011 kotun koli ta soke zdaben Mukhtar Idris na jam’iyyar APC ana ‘yan kwanaki da rantsar da shi a matsayin gwamna.
Haka kuma a watan Fabrairu na shekarar 2020 kotun koli ta soke zaben Dabid Lyon na jami’iyyar APC a matsayin gwamnan Jihar Bayelsa ana saura awa 24 kafin a rantsar da shi a matsayin gwamnan jihar.
Haka kuma a wani hukunci mai ban mamaki da kotun koli ta yanke a shekarar 2020 inda ta soke zaben Emeka Ihedioha na jam’iyyar PDP a Jiihar Imo inda ta tabbatar da zaben Hope Uzodimma na jam’iyyar APC a zaben da aka yi a ranar 9 ga watan Maris a fadin jihar.
A shekarar 2015, kotun daukaka kara ta soke zaben sabon Gwamna Nyesom Wike, inda ta tabbatar da hukuncin kararmar kotu, amma gwamnan na jam’iyyar PDP ya garzaya kotun koli inda ta tabbatar masa da hukuncin shi ya lashe zaben, abin da ya kawo karshen dambarwar da aka yi ta yi a fagen siyaasar jihar gaba daya.
Haka kuma a shekarar 2012 bayan babban zaben shekarar 2011, kotun koli ta kori gamnnonin wasu manyan jiohohi 5 saboda wa’adinsu ya kare tun a shekarar da ta gabata a ka kuma maye gurbinsu da shugabannin majalisar dokokin jihohin don su rike madafun iko.
Gwamnonin johohin Bayelsa, Kuros Riba, Kogi, Adamawa da Sokoto sun kama aiki ne a watan Mayu na shekarar 2007 amma kotun sauraren shari’a zabe ta soke zaben nasu saboda badakalar cuwacuwan zabe, kotu ta bayar da umarmin a sake zabe, amma kuma dukkan su suka sake lashe zaben da aka yi ba tare da wani wahala ba.
Bayan zaben shekarar 2007 kotun daukaka karar zabe ta kori wasu gwamnoni da suka hada da Olusegun Agagu na Jihar Ondo, Farfesa Oserheimen Osunbor na Jihar Edo, amma shari’ar Andy Uba na Jihar Anambra da Celestine Omehia na Jihar Ribas an cire su ne a hukuncin da kotun koli ta yanke a kan daukaka kara da aka yi a kan su.
Duk da cewa, masu fashin bakin harkokin siyasa za su iya hasashe yadda shari’ar za ta kasance a gaban kotunnan zaben a sassan Nijeriya musamman in aka yi la’akari da yadda shari’un suka kasance a shekarar 2023, amma a kwai wasu jihohi da ake sa ido a kansu saboda yadda shari’ar take, za kuma a iya samun ba-zata a shari’un da za a yanke a nan gaba.
Kotun sauraon kararrakin zaben gwamnan da ke zamanta a Jihar Kano bisa jagorancin Mai Shari’a Akintan Osadabay ta ci gaba da sauraron karar da Jam’iyyar APC ta shigar da ke kalubalantan zaben Gwamna da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris na 2023 da ya gabata.
Tuni bangarorin da ake karar suka kammala gabatar da shaidu da bayanansu ga kotun, a 20 ga watan Yuli 2023 da aka tsara domin wanda ake kara na farko hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa INEC ta fara gabatar da shaidar kariya, Lauyan hukumar zaben Barista Oshayomi Emmanuel ya bayyana wa Kotun cewa ba su da wata shaida da za su gabatar gaban Kotun, don haka suka rufe kariya gaban Kotun.
Lauyan Gwamna Abba Kabir Yusuf, R A Lawal SAN da kuma lauyan jam’iyyar NNPP John Olusola SAN ba su kalubalanci INEC ba a kan rufe kariyar ta su.
Bisa hakan ne Maishari’a Akintan Osadebay ta dage sauraron shari’ar zuwa ranar Juma’a 21 ga watan Yuli 2023 domin bai wa wanda ake kara na biyu Injiniya Abba Kabir Yusuf damar fara gabatar da nasa shaidun na kariya a gaban Kotun. Kuma tuni suka kamala gabatar da shaidu da bauyana su a gaban kotun. A cikin mako mai zuwa ne ake sa ran kotun za ta yanke hukunci.
Masu lura da al’amurran siyasa na Jihar Kano suna da ra’ayin cewa, lallai akwai yiwuwar assaamu hukunci na ban mamaki a jihar Kano. A saboda haka a halihn yanzu ana nan ana jira ranar da za a yanke hukunci a kan shari’ar. Ko dai Gwamna Kabir ya ci gaba da mulkinsa ko kuma Alhako Yusuf BGanuwa ya samu damara darewa karagar mulkin, masu iya agana dai na cewa, ba a sanin maci tuwo msai miya ta kare
A Jihar Kaduna ma, Babbar Jam’iyyar adawa ta PDP a jihar ta kalubalanci ayyana Uba Sani a matsayin wanda ya lashe zaben da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta gudanar tare da dan takararta Mohammed Ashiru Isa, suna neman a sake sakamakon zabe.
A cikin karar da ake kalubalantar nasarar Uba Sani, masu shigar da kara sun kira shaidu 24 tare da gabatar da su a gaban kotu.
A ranar Litinin 4 ga watan Satumba, kotun sauraron karar zaben gwamnan Jihar Kaduna ta kammala amsar dukkanin shaidun da aka gabatar mata, wanda a yanzu ana jiran yanke hukunci ne kawai.
Kotun sauraron karar da ke karkashin mai ahari’a, Bictor Obiawie, ta yi alkawarin a kowane lokaci za ta yanke hukunc a nan gaba bisa adalci ga kowani bangare.
Ita ma hukumar zaben wadda ita ce farkon wacce aka shigar da koken a kanta, ta tabo batun wani kuskuren da masu shigar da kara suka yi kan amincewa da takardun zabe.
Bayan gabatar da jawabinsa na karshe a rubuce a gaban alkalan kotun mai mutum 3 karkashin jagorancin Bictor Obiawie, dan takarar PDP, Isah Ashiru ta bakin babban lauyansa, Oluwole Iyamu ya bayyana cewa INEC ce ta sauya sakamakon zaben.
Ashiru ya kuma yi zargin cewa an samu kuri’u da suka wuce ka’ida da kuma kin bin tsarin zabe, yayin da ya yi kira da INEC kar ta bayyana sunan Uba Sani a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Jihar Kaduna.
Jihohin sun kuma hada da Legas, Inugu, Ribas, Delta da Akwa Ibom.
A Jihar Legas, kotun saurarron karrarrakin zaben gwamna da na majalisar dokoki ta karbi korafe-korafe a kan zaben da aka gudanar na shekarar 2023, ta karbi korafi daga jami’iyyar PDP da dan takararta, Abdul-Azeez Adediran (Jandor); jam’iyyar LP da dan takararta Gbadebo Rhodes-Bibour; jami’iyyar APM da kuma jam’iyyar APP.
Wadanda ake kara a takardar karar jami’iyyar PDP da dan takararta Jandor sun hada da hukumar zabe INEC, Gwamna Babajide Sanwo-Olu, mataimnakin gwamna, Obafemi Hamzat, jami’iyyar APC, jami’iyyar LP da dan takararta Gbadebo Rhodes-Bibour.
Jam’iyyar PDP da Jandor na neman kotun sauraron karar ta soke zaben Sanwo-Olu da Rhodes-Bibour a kan rashin aiki da dokar zabe ta 2022 da kuma dokokin hukumar zabe INEC.
Bayan rashin aiki da dokokin zabe na shekarar 2022, Adediran ya kuma kara da cewa, a lokacin da aka gudanar da zaben Gwamna Sanwo-Olu, Hamzat da Rhodes-Bibour basu cancanci tsayawa takarar zabe ba.
Ya nemi kotu ta yi watsi da kuri’un da aka kada musu, ta kuma ayyana Adediran a matsayin wanda ya lashe zaben da aka gudanar.
Amma sunan jam’iyyar LP kawai aka ambata a takardar shari’ar amma ba a ambaci dan takararta Gbadebo Rhodes-Bibour ba, ba a kuma sanya sunan jami’iyyar a cikin jerin masu korafin ba.
Wadanda ake karar a takardar Rhodes-Bibour sun hada da INEC, Sanwo-Olu, Hamzat da kuma jam’iyyar APC.
Yana neman kotu ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben saboda Sanwo-Olu bai cancanta da tsayawa takara ba tun da farko.
Amma ita jam’iyya LP ta tsaya a kan cewa, zaben Sanwo-Olu’s bai dace ba saboda cuwacuwar da aka tafka da kuma yadda aka kaucewa dokokin zaben shekarar 2022 da tsarin mulkin shekarar 1999.
Rhodes-Bibour ya kuma bayyana cewa, ba kuri’un masu zabe da suka yawa suka gudanar da zabensa ba.
A Jihar Ebonyi kuma INEC ta ayyana dan takarara jam’iyyar APC, Hon Francis Ogbonna Nwifuru, a matsayin wanda ya lashe zabe gwamnan da aka yi.
Dan takarar jam’iyyar PDP, Dakta Ifeanyichukwuma Odii, tare da na jam’iyyar APGA, Farfesa Ben Odoh, sun garzaya kotun zabe inda suka kalubalanci zaben da aka yi wa dan takarar jam’iyyar APC suna zargin ba a bi dokokin zabe na shekarar 2022 ba an kuma takura wa masu kada kuri’a tare da kasa aika sakamakon zabe ta na’ura mai kwkakwalwa da saura wasu korafe-korafe.
‘Yan takarar jam’iyyar PDP da na APGA sun yi korafin cewa, Nwifuru bai cancanci ya tsaya takara ba don shi ba cikakken dan jam’iyyar APC ba ne, shi dan jam’iyyar PDP ne a lokacin da aka yi zaben fidda gwmani. ‘Yan takarar gwamnan sun nufi kotun zaben inda suke neman a soke takarar Nwifuru saboda rashin cika dokokin zabe da suka hada da rashin sauka daga kujerarsa na shugaban majalisa a lokacin da ya tsaya takarar gwamnan.
A Jihar Ribas kuwa, dan takarar gwamna na jam’iyyar APC da LP, Tonye Cole, da Beatrice Itubo, suna kalubalantar zaben 2023 da ta kai ga fitar da Gwamna Siminalayi Fubara na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zabe.
Dan takarar jam’iyyar SPD, Sanata Magnus Ngei Abe, ya janye kararsa a kotun sauraren karar zaben jihar Ribas da ke zama a Abuja.
Amma daga dukkan alamu dan takarar gwamna na jam’iyyar APC, Cole, bashi da goyon bayan shugabannin jam’iyya na kasa musamman saboda hadin gwiwar da ke tsakanin shaugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ministan Abuja, Nyesom Ezenwo Wike a kan haka suka janye karar da suka kai kotun zaben.
A Jihar Inugu, Gwamna Peter Mbah na fuskantar shari’ar da ta dauki hankalin al’ummar Nijeriya wanda hakan kuma yana kara haifar masa da karin matsaloli.
Wanda ya shigar da karar, Chidioke Edeoga na jam’iyyar LP, ya yi zargin cewa, gwamnan yana mafani da takardar NYSC na bogi ne. Na biyu kuma yana zargin ba a yi amfani na na’urar BBAS ba a zaben da aka gudanar a wasu wuraren, ya kuma zargin wasu kuri’un da ya nlashe ba a bashi ba an karkatar da su.
Haka kuma a Jihar Abia, zaben da aka yi wa Aled Otti na jam’iyyar LP na fuskantar kalubale daga Ikechi Emenike na jam’iyyar APC, da kuma Okey Ahaiwe na jam’iyyar PDP.
Takardar karar Emenike a kan gwamnan ya shafi yadda gwamnan bai fita daga wata jam’iyya ba kafin ya shigo jam’iyyar da ya yi wa takara ta LP.
Ya kuma bayyana cewa, babu sunan Otti a kundin rajistar jam’iyyar LP kafin a zaben fidda gwani na takarar jam’iyyar LP.
Haka kuma, hukumar zabe INEC ta ayyana Gwamna Umo Eno na Jihar Akwa Ibom a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna da aka yi an kuma rantsar da shi a matsayin gwamna jihar a ranar 29 ga watan Mayu 2023 duk kuwa da korafe-korafen da aka yi a kan zaben nasa daga jam’iyyun hamayya.
Jam’iyyu hamayya sun yi korafi a kan cancantar Eno na tsayawa takarar zaben suna kuma zargin sa da amfanbi da takardar makaranta ta bogi, jirkita shekarun haihuwarsa da kuma magudin zabe da aka tafka.
Tsohon sakataren jam’iyyar APC, Sanata John Akpan Udoedehe, wanda a yanzu ya koma jam’iyyar NNPP; tsohon sanata, mai wakiltar Akwa Ibom ta arewa, Senator Bassey Akpan, na jam’iyyar YPP da Ezekiel Nya-Etok na jam’iyyar ADC suke kalubalantar yadda aka gudanar da zaben a gaban kotu.
LEADERSHIP Hausa ta gano cewa shugaban kotun sauraron karar, Maishari’a A. A. Adeleye na gab da bayyana hukuncin shari’ar musamman ganin dukkan bangarorin sun kammala gabatar da bayanai da hujjojinsu. Tabbas a ‘yan kwanakin nan kallo ya koma kotunan sauraron kararrakin zaben gwamnoni domin ganin yadda za ta kaya.
…Zaben Gwamnan Taraba: Cikin Matsi INEC Ta Ayyana Sakamako, A Sake Zaben Kawai – NNPP
Kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan Jihar Taraba da ke zamanta a Jalingo, ta ce za ta yanke hukunci kan karar da dan takarar jam’iyyar NNPP, Farfesa Sani Yahya ya shigar, yana kalubalantar nasarar Gwamna Agbu Kefas, na PDP a zaben 2023.
Babban Lauyan jam’iyyar NNPP, Barista Ibrahim Isiyaku (SAN), ya nemi a sake duba sakamakon zaben, inda ya nanata cewa, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bayyana sakamakon zaben ne bisa tsoro da tilastawa.
Kotun ta kebe ranar da za ta yanke hukunci ne biyo bayan karbar takardun korafe-korafe da hujjoji daga bangarori biyun.
Barista Ibrahim Isiyaku (SAN), ya yi zargin cewa an samu rashin tantance masu kada kuri’a a lokacin zabe a wasu rumfunan zabe da aringizon kuri’u da sauya sakamakon zabe da dai sauran kura-kurai.
Ya nanata cewa, bisa wadannan kura-kurai da aka samu lokacin zaben, ya ba su damar neman garzaya kotu domin soke sakamakon zaben.
Barista Isiyaku ya kara da cewa, tun da farko, hukumar zabe a jihar ta amince a cikin rahotannin da ta bayar cewa, aikin zaben ya fuskanci kalubalen tashe-tashen hankula sakamakon harbe-harben bindiga da sojoji da ‘yansanda suka yi.
Shi ma da yake zantawa da manema labarai, Lauyan Hukumar INEC, Barista Emeka Okoro, ya ce, sun shaida wa kotun cewa, NNPP ba ta gabatar da wasu kwararan hujjoji da za su tabbatar da korafe-korafenta ba. Don haka, sun bukaci kotun da ta yi watsi da karar da jam’iyyar NNPP ta gabatar a gabanta.