Bisa illolin da sauya sabbin takardun kudaden da babban bankin Nijeriya CBN ya yi, gwamnatocin jihohin Kaduna, Zamfara Kogi sun maka gwamnatin tarayya a gaban kotun koli, inda suka bukaci da a dakatar da CBN daga wanzar da wannan sabon tsarin.
A cikin takardar karar wacce lauyan gwamnonin, Abdulhakeem Uthman Mustapha (SAN) ya shigar a gaban kotun a madadin gwamnonin, ya roki kotun da ta dakatar da gwamnati da babban bankin kasa CBN da bankunan kasuwanci da kungiyoyin hada-hadar kudi kan daina amsar tsaffin kudaden daga ranar 10 ga watan fabrairun 2023.
kwamishonin shari’a na jihohin ne suka shigar da karar yayin da babbar lauyan gwamnati kuma ministan shari’a shari’a, Abubakar Malami (SAN) ke kare wa gwamnatin tarayya.
Masu karar sun ce, tun daga lokacin da aka sanar da tsarin na sauya kudaden, al’ummomin jihohinsu suke fuskantar karancin sabbin takardun kudaden.
A cewarsu, wa’adin kwanuka goma da gwamnatin tarayya ta kara na kai tsaffin takardun kudaden ga bankuna sun yi kadan wajen magance kalubalen da tsarin ya haifar.
Sun bukaci kotun da ta dakatar da gwamnatin wajen yin amfani da CBN wajen ci gaba da wanzar da tsarin, inda suka yi nuni da cewa, tsarin ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar na 1999 da aka sabunta da kuma dokar CBN ta 2007 da kuma sauran dokoki akan maganar.