Yayin da annobar COVID-19 ke ci gaba da yaduwa a sassan duniya, hadin gwiwar samar da allurar rigakafi tsakanin Sin da kasashen Afirka, ta samu ci gaba mai ma’ana.
Tun bayan da aka gudanar da taron ministoci karo na 8 na dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka (FOCAC) a watan Nuwamba na shekarar 2021 ya zuwa wannan lokaci, kasar Sin ta samar da alluran rigakafin COVID-19 miliyan 189 ga kasashen Afirka 27, kana karfin samar da alluran tare da hadin gwiwar kasashen Afirka a cikin gidan kasashen, ya kai kusan allurai miliyan 400 a duk shekara.
Jami’i a hukumar raya hadin gwiwa ta kasa da kasa ta kasar Sin Liu Junfeng ya bayyana cewa, tun bayan taron ministoci karo na 8 na dandalin FOCAC ya zuwa yanzu, kasar Sin ta tallafa wa kasashen Afirka wajen yaki da cutar, tare da farfadowa da bunkasuwarta bayan barkewar annobar, ta hanyar aiwatar da ayyukan ba da taimako.”
Bugu da kari, a farkon shekarar 2023 ne, ake sa ran kammala aikin gina hedkwatar cibiyar yaki da cututtuka ta Afirka da kasar Sin ta ba da taimako. Matakin da ake fatan zai saukaka hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka a fannin kiwon lafiyar jama’a, da taimakawa nahiyar Afirka wajen inganta karfinta na rigakafi da shawo kan cututtuka.
Liu ya kara da cewa, kasar Sin za ta ci gaba da samar da alluran rigakafi da kayayyakin yaki da annobar ga kasashen Afirka dake bukata, da gudanar da hadin gwiwa a fannin likitanci da fasaha, da taimakawa kasashen Afirka wajen kyautata tsarin kiwon lafiyar jama’a, da tallafawa kasashen Afirka a yakin da suke yi da annobar COVID-19, da raya tattalin arziki da zamantakewa bayan barkewar annobar, da ba da gudummawa yadda ya kamata, wajen gina al’ummar Sin da Afirka ta kut da kut mai makomar bai daya.(Ibrahim)