Daga Kabir Yusuf
09132880426,
Munayya ta kasance wacce ta gina rayuwarta bisa dabi’ar karatu hakan ya sa tana sayen littafai a duk sadda take da kudi domin amfanin kanta. Cikin littafan da take yawan saye akwai na ilimin zamani da na kissoshin annabawan Allah da salihan bayi nagari. Galiban tana karanta littafan hikayoyi da kissoshi fitaccen marubuci kuma dan jarida mai suna Adamu Muhammad (Adamun Adamawa) yake rubutawa musamman ma na auratayya da zamantakewa ta fi nacin karanta su.Haka a bangaren labarai ma tana bibiyarsu tamkar wata ‘yar Jarida domin kuwa tana yawan sauraron gidan rediyon BBC Hausa. A bangaren gidajen Talabijin kuma tana kallon gidajen Talabijin da suka hada da Aljazeera,CNN.A bangaren jaridu kuma tana karanta Daily Trust, Blue Print, Leadership, Almizan, Aminiya galiban tana samun su ne ta PDF hakan ya sa tana da sanayya dangane da siyasar Duniya.Wannan tsokaci dangane da karatunta kenan.
Munayya sun dauki sati biyar suna gabatar da jarabawa daga karshe zangon karatu na farko.A wata ranar Alhamis ta yi sallama da abokin Mahaifinta da matarsa Hajiya Zainab ta tafi gida domin yin hutun zangon karatu na biyu.
Ta isa gida lafiya cikin koshin lafiya da nutsuwa a yayin da ta samu ‘yan gidan cikin lafiya da farin ciki.
BAYAN HUTU A GIDA
A wata ranar Litinin bayan ta yi sallar Asubahi sai ta je wajen Mahaifinta domin ta gaida shi,sai ya ce akwai wata muhimmiyar magana da yake so su yi.
Mal.Kabir ya kalli Munayya sannan cikin tausayi irin na Mahaifi ga diyarsa sannan yace,naso tun kafin ki zo hutu na buga miki waya dangane da maganar,amma yanzu babu matsala tun da ga ki gani.Maganar ita ce,tun da yanzu kin kusa kammala Makaranta bai fi saura wata 6 ba,ya kamata in san da wane saurayin kike tare a yanzu,domin nasan kila ba za a rasa wanda ya bayyana miki so ba ko?”Domin kuwa kima da darajar mace shi ne gidan mijinta.Bugu da kari, hakkin ne da ya rataya a wuyana in aurar da ke a sadda kika kai munzalin aure.
Cikin yanayi na jin kunya tattare da da sada kai kasa ta ce,eh Abbana ina da saurayi a nan garin Roni yake a unguwar Jataka sunan shi Haidar Ahamad.Sai Mal.Kabir yace,okey,na fahimta lallai na gane shi,yaro ne na kirki mai halayen dattijantaka,ban taba jin wani mummunar magana a kan shi ba.Madamar kin tabbatar da ce wa,ya kwanta miki a rai,kina son shi yana son ki insha Allahu babu matsala.Nagartar halayensa na cikin dalilan da suka sa na yi saurin aminewa da shi.Annabi Muhammad (s) yace,”Idan wanda kuka yarda da halayensa da dabi’arsa ya zo neman auren diyarku to ku aura masa.Idan kuka ki aikata haka to fasadi da barna za ta yawaita a doron kasa”.To tun da na yarda da nagartar halayenshi ba matsala ni dama burina ki auri mutumin kirki wanda zai kasance miki miji,uba,aboki,mai share hawaye ko da bayan babu raina.Ni nagarta ce farkon abunda nike dubawa kafin duk wadansu ababen la’akari su biyo baya.
Munayya tana zaune kusa tattare da Mahaifinta cikin nutsuwa sai ya ci gaba da maganarsa cewa,”Munayya duk da Mahaifiyarki Allah ya yi mata rasuwa,amma ina jin tamkar ina tattare da ita a ruhina.Tabbas na ji dadin zama da ita,ta yi matukar kyautata mini,hakan ya sa kullum nike kukan rashinta a zahiri da badini.A kan Mahaifiyarki Raihanat ne kara gaskata Hadisin Annabi Muhammad (s) da yace,”hakika Duniya abar jin dadi ce mafi alkairin jin dadi a cikinta ita ce mace ta gari”.A sadda kina karama kafin ta rasu ta yi mini wasiyya a kan in zamanto miki madadinta,kuma insha Allahu zan aikata hakan bi’iznillahi ta’ala.Zan ci gaba da kula da ke har karshen numfashina.Don haka ki gaya wa Haidar cewa,ya shaidawa iyayensa cewa,ina so su zo mu yi magana a tsakaninmu dangane da alakar da ke tsakaninku.
Bayan Munayya ta fita daga wajen Mahaifinta sai ta shaidawa Haidar ta waya sakon Mahaifinsu.Haidar ya yi matukar farin ciki da hakan.Bayan sallar La’asar ya zo gidan,sannan ta kara shaida masa sakon Mahaifinsu baki-da-baki.Bayan Haidar ya koma gida sai ya shaidawa Mahaifinsa maganar,a yayin da Mahaifinsa Mal.Ahamad ya amince tattare da sanya albarka a a kan maganar,ya kuma yiwa Haidar alkawarin ce wa,zai aika mutane gidansu Munayya domin ayi maganar aure.Bayan kwana biyu wakilan Haidar sun je gidansu Munayya a yayin da suka yi doguwar tattaunawa da Mahaifin Munayya da ‘yan uwansa.An yi maganar sa ranar aurensu wata 6 masu zuwa wanda ya kama watan Jimada Sani kenan.Dukkanin bangarorin sun ji dadin tattaunawar.An sa rana,an bayyana sadakin da za a bayar tattare da rabawa dangi da abokanen arziki goro da alawar baiko.
JARABAWAR MUNAYYA DAGA MATAR MAHAIFINTA
Lantana ita ce kishiyar Mahaifiyar Munayya wacce take matukar takura mata da cutarwa kala-kala tun sadda Mahaifiyarta Raihanat tana da rai.Amma kuma a duk sadda ta shirya wata makida sai Allah ya kare Munayya daga sharrin wannan matar.A wata rana daga cikin ranaku sai ta kira Munayya zuwa dakinta ta bayyana mata cewa:”hakika ni bana kaunar ci gabanki kuma da sannu zan sanya son da Mahaifinki yake yi miki ya zamanto kiyayya”Cikin yanayi na tausayi Munayya tabar wannan dakin a yayin da hawaye ke neman kwaranyowa daga idaniniyarta.A duk unguwar an riga ya da sanin munanan halaye na Lantana.Ta kasance mai son abun Duniya da fafutikar ta ruwa a jallo ba tattare da banbamce halas da haram ba wajen kayan sana’ar da take sayarwa a unguwar.Babban abunda ya sa mutane suke kauracewa yin mu’amala da ita shi ne,rashin tausayinta,dogon burinta ga kuma rashin rikon amana ta yadda da zaran an kawo mata ajiyar kudi take kashewa sannan sai an kai ruwa rana take biya.
Bayan fitar Munayya daga dakin Lantana sai ta shiga dakinta ta fara kukan wannan azaba da takurawar da matar Mahaifinta take yi mata.A gefe guda kuma ta tuna yadda take kyautata mata ta hanyar taya ta ayyukan gida kamar dafa abinci,wanki,shara amma duk ba ta gani.Mal.Kabir bai dawo gida da wuri ba a ranar sai da misalin karfe 5:00pm,shigowarsa gidan ke da wuya sai ya leka dakin Munayya sai ya same ta cikin yanayi na damuwa da bakin ciki hakan kuwa ya tayar masa da hankali sosai da sosai.Sallama ya yi sannan ya zauna a kan kujerar da ke dakin ya tambaye ta mi ya faru ne bayan baya gida?”Sai ta yi shiru na tsawon lokaci sannan ta ce,babu komai”Sai ya kara tambayarta Munayya mike faruwa ne don Allah ki sanar da ni matsalarki idan ba ki bayyana mini matsalarki wa za ki bayyanawa?”Sai ta bayyana masa irin dangogin gallazawar da matarshi take yi mata”Sai ya ba ta hakuri sannan ya nemi da ta tashi ta tafi Makarantar Islamiyyar da suke yi”Sannan ya fita daga dakinta.
Fitarsa ke da wuya ba ta tsaya ko’ina ba sai dakin Lantana ya yi sallama sannan yace da ita:Mi ya sa kike takurawa Munayya?”Sai Lantana tace,”mi tace maka na yi mata?”Sai yace,koma minene kika yi mata ai kin fi kowa sani”Sannan ya gargade ta da cewa,zalunci haramun ne a Musulunci. Kuma bai kamata idan zamantakewa ta hada ta da mutane ba ta rika cutar da su ba”Budar bakinta ke da wuya sai ta yi subul da baka ta ce,”Da sannu zan yi maganin irin wannan madarar kaunar da kake nunawa Munayya”Sai ya ce, da ita:a gabana kike bayyana haka?”Sai ta yi shiru shi kuma sai ya fita cikin fushi.