Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya bayyana jin dadinsa da kammala jigilar maniyyatan bana fiye da 4,000 zuwa kasar Saudiyya a bana.
Kashi na karshe na maniyyata fiye da 300 sun tashi ne tare da Amirul Hajj na jihar kuma Sarkin Lere, Sulaiman Umar, da sauran jami’ai.
- ‘Yansanda Sun Cafke ‘Yan Bindiga 4 A Kaduna
- Tsaro: Majalisar Ɗinkin Duniya Ta Shirya Taron Masu Ruwa Da Tsaki A Zamfara
Gwamnan ya yabawa jami’an hukumar jin dadin alhazai ta jihar bisa jajircewarsu wajen ganin an samu nasarar aikin hajjin 2024, inda ya bukace su da su tabbatar da cewa, mahajjatan sun ci moriyar kudinsu a lokacin zamansu a kasar Saudiyya.
Amirul Hajj ya mika sakon yabon gwamnan ne a lokacin da yake mika sakon bankwana ga rukunin karshe na alhazan jihar a sansanin alhazan Mando ranar Litinin.
Ya ce, gwamnan ya yabawa jami’an hukumar bisa samun matsugunai masu kyau ga alhazai bisa la’akari da mafi kyawu, inda ya ce, da yawan sauran jihohin sun yi koyi da hakan.