…Haka Dai Aka Yi Bubukuwan Babbar Sallah A Katsina

Sallah Biki Daya Rana

Daga El-Zaharadeen Umar Katsina 

Kamar kowace shekara, a bana ma cikin ikon Allah ya kaddara al’ummar Musulmi sun shaida bukukuwan Sallah Babba a Najeriya da kuma duniya baki daya.

Hakika kowace sallah  tana zuwa da salo da kuma darasi wanda ka iya zama izna a rayuwar dan adam, to haka abin yaka a wannan Sallah domin dai abubuwan da aka shaida a wasu wuraran sai dai ace Allah sam barka.

Yanayin da al’umma ta tsinci kanta sai godiyar Allah domin hakan ne ya samar da wani yanayi da wannan sallah ta zo a ba zata, wasu sun yi salamun salamu, wasu sun yi ta da kyar wasu kuma sai a hankali.

Bari mu duba wasu abubuwa da suka haifar da wadannan matsaloli da ‘yan Najeriya ba za su sake fatan Allah Ya maimaita irin haka ba, sai dai wata kaddarar ubangiji.

A wannan lokacin da ake cikin yin bubukuwan Sallah Babba wanda ita ce ga al’adar Malam Bahaushe bai cika yin sabin dinki ba, sai dai ya wanke na karamar Sallah ya maida abinsa ya yi fuska, ya yi shagalin bikin Sallah lafiya.

Banda wannan matsalar wanda daman an saba da ita, yanzu sabuwa fil sun kara kwararuwar cikin wannan al’umma wanda ya hana mata sakat wajen gudanar da sauran al’amara cikin kwanciyar hankali.

Abincin da Bawa zai kai a bakin salatinsa ya zama jan aiki balanta Layya ko wasu hidimomi da bukukuwan Sallah ke samar da su, idan kuwa ba a ci abinci ba, babu yadda za a yi sauran al’amuran su tafi daidai.

Rashin zagawar kudi a tsakanin al’umma ya haifar da wani mummunar yanayi da ake kira “Bawa kusa da kushewa” wato dai duk lokacin da wani  abu ya tasowa Bawa zai iya cimmasa saboda baya da kariya sai Allah.

Idan masu abin hannu ba su taimakwa talakwa ba wajan raba masu naman layya ba, hakika hana na iya jefa su cikin yanayin kwalama da ka iya haddasa daukar hankalin wanda ya ji kamshi, saboda yanayin da aka shiga na rashin abin hannu.

Idan ba a manta ba, tuni gwamnatin tarayya ta toshe kunnuwanta daga jin kuka ko korafin na kasa da ita domin kadda ma ta ji balanta ta taimaka masa, idan kuwa haka za a cigaba da zama lallai sakamakon ba zai yi kyau ba.

Tunda wannan gwamnatin ta shugaban Buhari ta hau mulkina shekara 2015, bata taba tausayawa ta yi wani abin a zo a gani ba, ga ma’aikata domin su yi shagulgulan Sallah cikin annashuwa da walwala ba.

Saboda haka kullin tunanin shi ne, gwamnati na iyakar kokarinta, kuma wai biyan albashi ba lokacinsa ba, baya daga cikin dokar kasa, wani lokacin suna daukar biyan albashin tamkar wani aikin bajinta ne da za a yi cewa gwamnati ta samu nasara.

Duk wani mutun mai nazari zai ga yadda mafiyawan al’umma suka yi wannan Sallah, musamman idan ya fara duba makusantarsa wato makwabta da sauran al’umma, sai kara gane irin halin da ake ciki na rashin da talauci da kuma shiga uku.

Dole a tausayawa wadanda ba su da shi, kuma idan akwai hali ya zama wajibi a taimaka masu da abinda za su ci su sha a dalilin wannan Sallah, daman kamar yadda na fada an bar maganar sabon dinki, magana ce ta me za aci, ba me za a sa ba.

Bukukuwan Sallah na daga cikin abubuwan da suke taimakwa wajan bunkasa tattalin arzikin ‘yan kasa musamman mutanen arewa wadanda ake bubukuwan Sallah a wasu garuruwansu da masarautunsu.

Saye da sayarwa da ke guduna a cikin kwanaki uku zuwa hudu na bukukuwan Sallah suna taimakawa matuka wajan samar da kudade a hannun jama’a wanda ta wannan hanyar ne suke kara bunkasa tattalin arzikinsu da kuma kasuwancin su.

Kuma hatta ita kanta gwamnati da kamfanoni da sauran al’umma suna dogara da wannan bukukuwa na Sallah domin samun abin kasuwa da kuma adanawa saboda gaba, wani lokaci ma yana zama sillar daukakar kasuwancinsu.

To amma duk lokacin da aka samu wata matsala da ta zama sanadi na hana wannan bukukuwan sallah a yankin arewa ba karin cikas da koma baya ake samu ba a fagen kasuwanci da bunkasar tattalin arziki ba.

Saboda haka wani abin mamaki yanzu shi ne yadda hukumomin ke rufe ido sun jefa jama’a cikin wannan halin da suke da masaniya game da shi, wanda a sanadiyar haka muna ganin irin abubuwan da ke faruwa na rashin da shiga halin kuncin rayuwa ga al’umma.

Yanzu dai muna gani, haka dai aka yi wannan Sallah babu wani armashi balanta kayatarwa, sakamakon soke duk wasu bukukuwan Sallah da ke taimakawa kanana da manyan ‘yan Kasuwa wajan bunkasa tattalin arzikinsu na yau da kullin.

Wannan yasa har gobe al’ummar Najeriya da yawansu ba su amince da wannan cuta ta korona ba, wanda a wannan shekarar ma da ita ne aka fake wajan dakatar da duk wasu shagulgulan Sallah Babba wanda haka idan ace masana tattalin arziki za su gudanar da bincike sun bada sakamako sai an yi kuka saboda abinda aka rasa.

Darasin rayuwa dai kullin yana bayyana sai dai wani lokacin dan adam na da mantuwa, da zaran an dauki lokaci sai ya manta da abinda ya faru, wannan kisan mummuken da ake yi masa ta hanyar hana bubukuwan Sallah domin jefe shi cikin hali, ya kasa gane haka.

Amma dai lokaci na kara karatowa, wanda za su yi amfani da shi wajan yakin neman zabe, ina da tabbacin cewa ba Korona ba,  ko wata cuta mai suna mutuwa zata bayyana a shekara mai zuwa ba za su sake fakewa da wannan  cutar ba wajan cutar da jama’a ba saboda biyan bukatar su ta kusa.

Da fatan Allah Ya karbi ibadunmu ya kawo mana saukin Rayuwa, ya sanya wannan ya zama darasi na gaba domin samun mafita ta rayuwar duniya da kuma lahira. Amin Summa Amin.

Masu karatunmu Barka da Sallah Da fatan Za a yi shagulgulan Sallah lafiya. Na gode

Exit mobile version