Nazir Alkanawy" />

Hankali Da Lura: Matsayinsu Da Muhimmancinsu A Rayuwar Hausawa

Rubutu Da Marubuta:

 Tare da Nazir Alkanawy 08035638216             imel: naziralkanawy@gmail.com

Dakta Hauwa Muhammad  Bugaje

Sashin Nazarin Harsuna Da Al’adun Afirka.

Jami’ar Ahmadu Bello Zariya.

 

Wannan wata mukala ce da Dakta Hauwa Bugaje, Malama a Sashin Nazarin Harsuna da Al’adun Afirka na Jami’ar Ahmadu Bello ta gabatar kuma aka buga a liitafin Champion of Hausa cikin Hausa, wanda Sashin Nazarin Harsuna da Al’adun Afirka ya wallafa domin karrama Farfesa Dalhatu Muhammad. Mun dauko muku wannan kasida ce saboda amfanin da masu karatu za su samu daga ilimin da ke cikinta. A sha karatu lafiya:

 

Hankali muhimmin abu ne a rayuwar dan’adam. Lura kuwa ba ta samuwa sai da hankali, kamar yadda rayuwa ba ta inganta sai da lura. Wannan mukala ta yi nazari ne a kan kyawawan dabi’un nan ne da aka san Bahaushe da su, watau hankali da lura. Sannin muhimmancin wadannan abubuwa masu alaka da juna ya sa aka zadi a rubuta wannan mukala a kansu, ba domin komai ba sai domin ganin yadda wadannan kyawawan dabi’u suke neman su yi karanci, a tsakanin al’umma musamman matasa. An yi sharhi ne ta hanyar kafa hujja daga taskar adabi, watau ta hanyar kawo misalai daga karin magana.

 

Gabatarwa

Hausawa kan ce “Yabon gwani ya zama tilas” , haka kuma su kan ce “Ba rabo da gwani ba kafin a mai da gwani” Tabbas wannan zance haka yake. A kullum nakan yi mamakin ni’imar da Allah ya yi wa wasu bayinsa kodayake ba mamaki da ikon Allah, amma abin da nakan duba daga irin wadannan bayin Allah shi ne, dabi’arsu da yadda suka dauki rayuwa da hanyoyin da suke tafiyar da al’umma a rayuwarsu. Hakika wanna baiwa ce da Allah ya yi wa shaihin malami Farfesa Dalhatu Muhammad, wanda malami ne da ya tattara siffofi abin a yi nazari da koyi musamman a wanna zamani na tsaka-mai-wuya.

Masana irinsu Kirk-Greene (1966) da Guga (2001) da Amina (2005) da Hadiza (2009) da Bugaje (2011) sun gudanar da nazarce-nazarce kan kyawawan dabi’un Hausawa. Suna “Mutumin kirki:  The concept of Good man in Hausa “ Ya bayyana matsayin mutumin kirki a Hausa inda ya kafa misali da wasu fitattun mutane a kasar Hausa kamar  Sarkin Musulmi Muhammadu Bello da sauransu. Ya bayyana yadda Bahaushe yake kalon mutumin kirki: da hanyar kafa hujja da karin maganar Hausa.

Guga(2001) a kundin bincikensa na digirin farko ya nazarci Tunanin Bahuashe a littafan gasa ta farko (1933). A cikin wannan aiki ya yi sharhi a kan  muhimmancin ilimi da gaskiya da amana da biyayya da hakuri da jarunta da kunya( da sauransu) kamar yadda aka fito da su a gasa ta farko.

Amina (2005) ta yi nazari  a kan Tasirin zamananci a kan  kunya, a kundin digiri na farko. A binciken na ta, ta yi bayanin kunya da muhimmancinta a al’adar Bahaushe, sannan ta yi nazarin yadda zamananci ya yi tasiri ga kunya inda ta bayyana cewa daga cikin abubuwan da suka yi wa kunya nakasu a yau akwai tasirin ilimin boko da samuwar fina-finai da sauransu. Kunya tana daga cikin dabi’un Bahaushe.

Hadiza(2007) ta yi nazari ne a kan Hakuri a Rubuce-rubucen Wasan Kwaikwayo. A aikin nata ta kawo muhimmancin hakuri a al’adar Hausawa da kuma yadda marubuta wasan kwaikwayo suka fito da jigon hakuri. Daga cikin littafan wasan kwaikwayo da aka nazarta akwai littafin wasan kwaikwayon Jatau na kyallu da Matar Mutum Kabarinsa da Uwar Gulma.

Irin wadannan ayyuka  na kara fito da daraja da kimar Hausa da al’ummarta, kuma yana sa Hausawa su san asalinsu da kyawawan dabi’un da suka gada. Haka kuma, masana da dama  sun yi nazarin karin maganar Hausa. Daga cikinsu akwai Hill (1972) da Garba (1982) da Zaruk da Alhassan (1982) da Bada (1995) da Fatima (2009) Da Lauratu (2011) da sauransu, wadanda dukkaninsu sun yi nazarin karin magana ne tsagwaronta. A yayin da ayyukan Edga(1913) Whitting (1940) Da Kraft (1966) da Skinner (1980) da sauransu. Suka yi tsokaci kan Karin magana a yayin da suke bayanin wasu nau’o’in adabi. Har wayau ayyuka irin na Adam (1994) da Amin (2002) da sauransu sun nazarci falsafa ne ta hanyar kafa hujja da karin magana.

Kirk-Greene(1966) ya bayyana cewa karin magana na inganta al’adun al’umma da suka gada da tarihin al’umma da hikimomin al’umma. Bayan haka,  a inda ba a samu rubutaccen adabai ba, karin magana na iya zama kafar tattara falsafar kasa.

Zaruk da Alhassan (1982:3) sun bayar da ma’anar karin magana da cewa nazari ne na rayuwa a dunkule, cikin gajerun maganganu da misalai irin na hikima. Karin magana ba ta faye zuga ko kuda ba, sai dai gwanintar kwatance, misali “Kome nisan jifa kasa za ta dawo”. Domin haka, a iya cewa nazari a fagen dabi’un Bahaushe, da kuma nazari kan Karin magana na samun kulawar masana da manazarta harshen Hausa.

Ma’anar Hankali

Kalmar hankali (a nahawance) kalma ce ta suna  wadda za ta iya tsirar da Kalmar aikatau, hankalta da kuma sifa, mai hakali. Don haka kalmar hankali, a iya cewa kalma cewa da ake iya gina wasu kalmomi daga gareta. Haka kuma kalmar hankali akasi ce ga kalmar hauka wadda ke nufin rashin hankali.

Bargery (1934) ya bayyana kalmar hankali da cewa, ta kunshi kalmomi kamar . hankali da lura, kwanciyar hankali kula da sauransu. Haka kuma marubucin ya bayyana  kalmar hankali da cewa ta kunshi hankalta, watau fahimtar abin da aka fada, sa’an nan ya kira mai fahimta da mahankalci.

A kamusun Hausa (2006) an bayyana hankali a mtsayin lura  da sanin yakamata da natsuwa da aiki sannu sannu  da sauransu. Haka kuma, a kamusun an bayyana hankali ya kunshi hankalta watau gane yadda ake aikata wani abu ko fahimta.

Idan aka yi la’akari da ra’ayoyin masana za a fahimci cewa hankali na nufin tsai da rai waje daya domin fahimtar wani al’amari da neman mafita. Haka kuma ana iya fahimtar abubuwa da ke kaiwa da komowa  a sararin duniya har da zabin abin da ya dace da rayuwa ta gari da gudanar da abubuwan da za su amfani al’umma na daga siffofin hankali da mai hankali. Yayin da aka samu akasin haka, watau mutum ya kasance ba ya iya tsai da ransa ya fahimci abu kuma ba ya iya rarrabe abin da ke kyautata rayuwa da wanda ke gurbatata da kuma kasa bambance abin da za ya amfani al’umma da wanda za ya cutar da ita, a nan akwai rashin hankali (hauka). Mai wannan dabi’a ake kira mahaukaci a Hausance.

 

Matsayin Hankali A Rayuwar Bahaushe.

Hankali na da matsayi mai girma a rayuwar Hausawa, domin yana daga sahun farko na kyawawan dabi’unsu wanda a da, da su ne suka yi fice har suka shahara a duniya. Haka kuma, hankali na matsayin fitila ga Hausawa wadda ta haska masu hanyoyin fatauci da kasuwanci da zamatakewa da shugabanci da yake-yake da sauransu. Akwau hanyoyi ko ma’aunai da ake auna hankalin mutum. Wadansu ma’aunan su ne, wasu daga cikin kyawawan dabi’u kamar natsuwa da hakuri  da gaskiya da kunya da biyayya da kawaici da dattako da sauransu. Wanda aka samu da wadannan dabi’u ya zama cikakken mai hankali, don haka za a iya sakar masa jagorancin jama’ domin an san za ya yi adalci da tausayi da kiyaye hakkin jama’a.

Za a iya fafahimtar matsayin hankalli a rayuwar Hausawa idan aka yi la’akari da wadannan karin magana.

Aiki Da Hankali Ya Fi Aiki Da Agogo

A zahirin ma’anar sarai a iya cewa wannankarin magana na nufin gudanar da aiki ta hanyar lura ya fi aikin da aka gudanar ta hanyar bin lokacin agogo. Sai dai a ma’anarta ta boye karin maganar na nuna matsayin hankali da cewa, kome mutum zai yi ya auna shi da hankalinsa ya ga dacewarsa da rashin dacewarsa, ba wai kawai ya gudanar da shi kai tsaye ba.

Hankali ya fi wayo

Ma’anar wannan karin magana a fili take watau mutum ya kasance mai yin abin da ya dace  a kowane lokaci, ba a bin da ya kwanta masa a rai ba. Domin wayo na daga son zuciya. Shi kuwa aikin da hankali na daga fin karfin zuciya domin gudanar da abin da ya dace.

Mai hankali ke gane dingishin kwado

A zahiri an san cewa abu ne mawuyaci a gane dingishin kwado, tun da shi tsalle yake ba tafiya ba. Amma abin da wannan karin magana ke nufi shi ne akwai wasu al’amurra masu muhimmanci a rayuwa da ba kowa ke iya gane su ba, sai masu hankali.

Za mu ci gaba a mako mai zuwa da yardarm Allah.

 

Exit mobile version