Hukumar Kula da Yanayi ta Kasa wato (NIMET), ta yi hasashen cewa; za a fuskanci tsananin zafin rana a shekarar 2025 a fadin Nijeriya, musamman a lokutan dare da kuma rana, inda kuma rana za ta yi dumi a watannin Janairu, Maris da kuma Mayu.
Haka zalika, Hukumar Kula da Yanayi ta Duniya (WMO) ta sanar da cewa, a shekarar 2024 ne, aka fi fuskantar tsananin zafin rana a cikin shekaru 175 da suka gabata.
- Yadda Tashar Jirgen Ruwan Apapa-Moniya Za Ta Taimaka Wa Masu Safarar Fitar Da Kaya
- NIMASA Za Ta Adana Wa Nijeriya Dala Biliyan 400 A Shekara Daga Cazar Kudaden Safarar Kaya
Kazalika, hukumar ta WMO ta yi gargadin cewa, shekarar 2025 za ta kasance mafi tsananin zafin rana.
Wannan karuwar tsananin zafin ranar, ba wai kawai za ta shafi amfanin gona ba ne, za kuma ta zama kalubale ga lafiyar kajin gidan gona.
Misali, kajin gidan gona masu saurin girma kamar samfurin da ake kira a turance da ‘Broilers’, na da gajeren lokacin jurewa zafin rana, musamman duba da cewa; ba sa iya jurewa tsananin zafin ranar.
Hanyoyi Biyar Da Mai Kiwon Kajin Gidan Gona Zai Kare Kajinsa Daga Tsananin Zafin Rana.
1- A Tabbatar An Sama Musu Wadacciyar Iska A Dakin Kwanansu:
Ana bukatar mai kiwon kajin ya tabbatar ya sama musu wadatacciyar iska a dakin kwanansu, ana kuma bukatar a yi wa shigifar dakinsu fenti yadda za ta rika rage zafin ranar da kuma samar da kayan koyon da za su sanyaya dakin kwanansu.
Haka kuma, ana bukatar a rika sanya musu na’urar da ke sanyaya daki, wadanda za su rika rage zafin ranar, akalla na’urar ta kasance mai ma’unin yanayi daga 5 zuwa 10°C.
2- Sanya Na’urar Sanya Daki:
Domin samun saukin yanayin zafin rana, ana bukatar mai kiwo ya sanya musu na’ura a dakin kwanansu, domin rika sanyaya dakin, yadda jikinsu zai rika yin sanyi.
Ana kuma bukatar masu kiwon, su rika sanya musu Fanka a dakin kwanansu, wanda hakan zai ba su damar samun wadatacciyar iska.
3- Shayar Da Su Wadataccen Ruwan Sha:
Tanadar musu da wadataccen ruwan sha, na taimaka musu wajen samun sinadaran da za su kara inganta rayuwarsu da kuma jurewa tsananin zafin rana.
Kazalika, ana bukatar masu kiwon su rika zuba musu garin sinadarin ‘glucose da amino acids’, domin kara musu karsashi da kuma kara karfafa garkuwar jikinsu.
4- Sama Musu Da Sauyin Ciyar Da Su Abinci:
Ana bukatar masu kiwonsu, su rika ciyar da su abinci mai dauke da sinadari kamar na ‘Bitamin E da selenium’, wadanda za su taimaka wa lafiyarsu.
Wadannan sinadarai, na matukar bayar da gudunmawa wajen ba su kariya daga jin tsananin zafin rana.
5- Sanya Ido Kan Yiwuwar Barkewar Wata Cuta:
Ana bukatar mai kiwon kajin ya tabbatar yana yawan sanya ido kan kajin, domin gano wasu alamomin da za su iya sanya su ji tsananin zafin rana ko kuma kamuwa da wasu kwayoyin cuta, musamman domin daukar matakan gaggawa na kare lafiyarsu.
Ana kuma bukatar mai kiwonsu ya tabbatar yana ciyar da su abinci mai gina jiki, wanda hakan zai taimaka musu daga saurin kamuwa da kwayoyin cututtuka.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp