• English
  • Business News
Saturday, October 25, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Har Kullum Kasar Sin Na Goyon Bayan Adalci Game Da Batun Falasdinawa

by CMG Hausa
3 years ago
Kasar Sin

Cikin tsawon lokaci, batun takaddamar yankuna tsakanin al’ummar Falasdinu da tsagin Yahudan Isra’ila na jan hankalin sassan kasa da kasa, musamman ganin yadda rashin warware batutuwa masu nasaba da mallakar yankuna tsakaninsu ke ta haifar da tashe-tashen hankula, masu kaiwa ga asarar rayuka.

Ko shakka babu, akasarin kasashen duniya na goyon bayan warware rikicin Falasdinu da Isra’ila, wanda ya samo asalin tun a tsakiyar karni na 20, ta hanyar kafa kasashe biyu masu cin gashin kansu, wadanda za su zauna da juna lami lafiya.

  • Har Yanzu Amurka Ba Ta Rabu Da Bukar Ba

To sai dai tsawon shekaru ke nan, wannan bukata ta gaza cimma nasara, duba da yadda manyan sassan dake da ruwa da tsaki, musamman ma Amurka mai da karfin fada a ji, ke nuna goyon baya ga tsagin Isra’ila, da yin watsi da matakan komawa teburin sulhu, hakan ya sa Ira’ila ke fakewa da wannan dama, tana fadada mamayar yankunan Falasdinu ba bisa ka’ida ba.

Duk da haka, a bangaren kasashen dake ci gaba da goyon bayan adalci, da biyayya ga manufofin MDD masu nasaba da wannan batu, kasar Sin ta jima tana jaddada muhimmancin tabbatar da daidaito da adalci, da fatan a komawa gudanar da shawarwari domin kawo karshen wannan sa-in-sa.

Ko shakka babu, matsayar kasar Sin na kan turbar adalci, ita ce kuma ta yi daidai da ra’ayoyin mafi yawan kasashen duniya, na kawo karshen rashin zaman lafiya da ya jima yana addabar wannan yanki na gabas ta tsakiya.

LABARAI MASU NASABA

Kasar Sin Ta Nemi Amurka Ta Dakatar Da Hare-haren Shafin Intanet Kan Muhimman Kayayyakinta Nan Take

An Kebe Ranar 25 Ga Oktoba A Matsayin Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

Duba da cewa, wannan batu ne mai dadadden tarihi, wanda kuma kai tsaye warware shi ke da alaka da wasu muhimman sassan kasa da kasa, fatan duniya a yanzu shi ne gwamnatin Isra’ila, da kungiyar PLO ta ’yantar da Falasdinawa, da masu shiga tsakani da suka hada da MDD, da Amurka, da Rasha, da tarayyar Turai, da kungiyar kasashen Larabawa ta LA da sauransu, za su rungumi matsayar kasar Sin ba tare da bata lokaci ba, ta yadda za a kawo karshen wannan takaddama ta Falasdinu da Isra’ila cikin ruwan sanyi.(Saminu Alhassan)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kasar Sin Ta Nemi Amurka Ta Dakatar Da Hare-haren Shafin Intanet Kan Muhimman Kayayyakinta Nan Take
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Nemi Amurka Ta Dakatar Da Hare-haren Shafin Intanet Kan Muhimman Kayayyakinta Nan Take

October 24, 2025
An Kebe Ranar 25 Ga Oktoba A Matsayin Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan
Daga Birnin Sin

An Kebe Ranar 25 Ga Oktoba A Matsayin Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

October 24, 2025
Sin Ta Saka Burikan Da Za Ta Cika A Shekaru 5 Masu Zuwa
Daga Birnin Sin

Sin Ta Saka Burikan Da Za Ta Cika A Shekaru 5 Masu Zuwa

October 24, 2025
Next Post
Mutane 8 Sun Mutu, 2 Sun Jikkata A Hatsarin Mota A Kogi 

Mutane 8 Sun Mutu, 2 Sun Jikkata A Hatsarin Mota A Kogi 

LABARAI MASU NASABA

Gwarzon Kamfanin Fasahar Kuɗaɗe Na Shekarar 2025, Opay Nigeria

Gwarzon Kamfanin Fasahar Kuɗaɗe Na Shekarar 2025, Opay Nigeria

October 25, 2025

Gwarzon Kamfanin Samar Da Kaya Na Shekarar 2025, Kamfanin Nestlé Pure Life

October 25, 2025
Mata Ne Ginshikin Ci-Gaban Al’umma – Gimbiyar Dange

Mata Ne Ginshikin Ci-Gaban Al’umma – Gimbiyar Dange

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Mawaƙin Shekarar 2025, Skales

October 25, 2025
Jami’ar ABU Ta Ƙaryata Zargin Ƙera Makamin Nukiliya A Asirce

Jami’ar ABU Ta Ƙaryata Zargin Ƙera Makamin Nukiliya A Asirce

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Hukumar Kare Ƴancin Masu Amfani Da Kaya (FCCPC): Tabbatar Da Adalci A Kasuwa

October 25, 2025
Fiye da Janarori 50 Za Su Yi Ritaya Bayan Sabbin Naɗe-Naɗen Tinubu

Fiye da Janarori 50 Za Su Yi Ritaya Bayan Sabbin Naɗe-Naɗen Tinubu

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Ma’aikacin Banki Na Shekarar 2025 Dakta Tony Okpanachi

October 25, 2025
Muna Duba Ƙudirin Ƙirƙiro Jihohi 55 – Barau Jibrin

Muna Duba Ƙudirin Ƙirƙiro Jihohi 55 – Barau Jibrin

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Shugaban Kamfani Na Shekarar 2025 Gbenga Olu Komolafe

October 25, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.