A yau Laraba ne cibiyar binciken harkokin ci gaba dake karkashin majalisar gudanarwar kasar Sin, ta fitar da rahoton ci gaban kasar na shekarar nan ta 2026. Rahoton da ya yi duba na tsanaki dangane da sabbin nasarori da aka cimma, a matakan ingiza zamanantar da kasar Sin, tare da lasafta jerin gudunmawar Sin ga ci gaban duniya baki daya.
Game da hakan, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun, ya ce har kullum Sin na sanya ci gaban kanta a matsayin damar bunkasa duniya baki daya, tana kokarin cimma moriyar bai daya, da samar da ci gaba ga kowa, kana tana amfani da zarafinta na zamanantarwa wajen ingiza sauran kasashe, ta yadda za su cimma nasarar zamanantarwa tare.
Guo ya kara da cewa, ci gaban Sin bisa babban matsayi yana samar da damarmakin bunkasa duniya baki daya. Ya ce Sin ta kasance hedkwatar manyan rukunonin kirkire-kirkire 25 cikin 100 mafi girma a duniya, kuma kirkire-kirkiren kimiyyarta sun samarwa karin kasashen duniya kafa, ta cin gajiyar fasahohin zamani da hajoji masu rahusa, tare da samar wa dukkanin kasashe da wani tsani na kaiwa ga nasarorin dijital.
Daga nan sai jami’in ya ce Sin na bunkasa tsarinta na bude kofa bisa babban matsayi, ta hanyar gudanar da bikin baje kolin kasa da kasa na hada-hadar shigar da hajoji sassan duniya, da baje kolin kasa da kasa na cinikayyar hidimomi, da baje kolin kasa da kasa na cinikayyar fitar da hajoji, da baje kolin kasa da kasa na shigo da hajoji, inda take samar da wasu damarmakin kasuwa mai fadi, da ikon zuba jari ga kasashen duniya. (Saminu Alhassan)














