Wasu daga cikin jama’ar da suka halarci ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen Shugaba Bola Tinubu na 2027 a Kaduna a ranar Asabar sun yi masa ihun “Ba ma yi,” ma’ana ba sa goyon bayansa.
Lamarin ya faru ne a filin wasa na Ranchers Bees, lokacin da Tinubu ya ce “Nijeriya” yana jiran jama’a su amsa.
Sai dai wasu daga cikinsu sun mayar da martanin cewa “Ba ma yi.”
Haka kuma, jama’ar sun ba da amsa daban lokacin da ya ambaci sunan Kaduna.
Wasu daga cikin waɗanda suka halarci taron sun shaida wa Aminiya cewa rashin tsaro da tsadar rayuwa ne suka sa suke nuna rashin jin daɗinsu.
A jawabinsa, Tinubu ya amince cewa yunwa ta addabi ’yan Nijeriya, amma ya ɗora alhakin hakan a kan ’yan adawa, tare da alƙawarin magance matsalar idan aka sake zaɓensa a 2027.
Gwamnonin jihohin Arewa maso Yamma guda bakwai, da wasu gwamnonin jihohi, manyan jami’an APC da ’yan Majalisar Dokoki ta Ƙasa sun halarci taron.
Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya miƙa tutocin jam’iyyar ga gwamnonin Arewa maso Yamma guda bakwai.













