Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume, ya ce duk wani ɗan Arewa da ke neman tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027 yana aiki ne a kan muradun yankin Arewa.
Akume ya bayyana hakan ne a wani taro da aka gudanar a Kaduna ranar Asabar, inda ya buƙaci ’yan Arewa su goyi bayan sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027, su kuma jira zuwa shekarar 2031 kafin su nemi shugabancin ƙasar.
Ya ce Tinubu ya yi wa Arewa adalci wajen naɗa mutane a muƙaman gwamnati da kuma ayyukan raya ƙasa.
Ya kuma yaba wa shugaban ƙasar bisa tallafa wa ayyukan ci gaba a Jihar Benue da sauran sassan Nijeriya.
Akume ya yi gargaɗin cewa burin siyasar wasu mutane na iya raba kan ’yan Arewa tare da rage tasirinsu a siyasar ƙasa.
Ya buƙaci su kasance masu haɗin kai tare da goyon bayan Tinubu a zaɓe mai zuwa.
Ya kuma yi kira ga magoya bayansa da su goyi bayan Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, domin ya sake komawa kan mulki, yana mai yaba wa jagorancinsa da ayyukan da ya gudanar.














