Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya ƙaddamar da kwamitin mutane 35 domin rabon tallafin ga waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri ranar 10 ga Satumba.
Ambaliyar ta haifar da babbar ɓarna, inda ta raba dubban mutane da gidajensu tare da lalata kayayyaki da gonaki masu yawa.
- Jarumai A Masana’antar Kannywood Sun Jajanta Wa Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Maiduguri
- Zamfara Ta Bayar Da Gudunmawar Miliyan 100 Ga Waɗanda Ambaliya Ta Shafa a Borno
Da yake jawabi a wajen kaddamarwar da aka yi a Fadar Gwamnatin Borno a Maiduguri, Zulum ya jaddada muhimmancin gaskiya da adalci a aikin kwamitin. Ya yi kira ga mambobin kwamitin su gudanar da aikinsu da amana, tare da tabbatar da cewa kowace Naira da aka ware don tallafi ta kai ga waɗanda abin ya shafa.
Gwamnan ya kuma sanar da cewa za a raba jimillar Naira biliyan 4.4 da aka samu a matsayin tallafi ga waɗanda ambaliyar ta shafa. Ya bayyana cewa ba daga cikin kuɗaɗen tallafin za a biya kudaden alawus ɗin mambobin kwamitin ba, sai dai daga asusun gwamnatin jihar. Har ila yau, Zulum ya tabbatar wa da jama’a cewa gwamnati za ta gyara kayayyakin more rayuwa da ambaliyar ta lalata.
Ya kuma bayyana cewa kawo yanzu an samu Naira biliyan 4.4 a asusun tallafin jihar, tare da alkawarin jimillar Naira biliyan 13.2, yana mai alƙawarin cewa za a yi bayani a bainar jama’a kan yadda za a raba waɗannan kuɗaɗen.