Har Yanzu Ni ‘Yar Koyo Ce A Harkar Fim, Inji Zahra’au Sale Fantami

A cigaba da kawo muku tattauawar da Wakiliyarmu RABI’A SIDI B. ta yi da tauraruwa a shirin nan na ‘Dadin Kowa’ wato ZAHRA’U SALE FANTAMI wadda aka fi sani da ADAMAN KAMAYE, a wannan makon ta tabo al’ummarra da dama wadanda suka shafi rayuwarta a masa’anantar kannywood, ga dai yadda hirra ta kasance:

A cikin shirin Dadin Kowa ana jinki da karin magana kala-kala, shin saka ki ake kiyi su, ko kuwa ke kike sakawa dan karawa shirin armashi?

Akwai ta su gaskiya akwai kalmominsu, amma muna dan jefa namu saboda mu muna tare da tsofaffi kuma mun taso a cikinsu, mu iyayenmu na fada miki kanawa ne, kin san hausa dai iya kar hausa kano, ba su yar da kanoncin nan ba dai mu shi suke mana domin shi suka gada kuma shi suka iya, toh anan muke samun karin magana da wani launin zance dai haka dai, gaskiya muna kari sosai, muna gyara musu in mun ji kalma ta yi dai-dai da abinda ‘dialogue’ din yake nufi, kalmar in ta yi dai-dai ba ta saba da abinda suke bukata ba toh muna dorawa wannan ba matsala bane muna kari sosai muna karawa in mun ga bai saba da hankali ba.

Wanne abu ne ya fi birgeki a shirin Dadin Kowa da ki ke yi, wanne waje kika fi so?

Ni a cikin shirin Dadin Kowa hausa sun ce wai a ruwan zafi ba gefe ko?, an ce a ruwan zafi duka ba gefe wallahi duk binda na yi a cikin shirin Dadin kowa yana birgeni, dalili kuwa ni cikin jin dadi nake ko me aka sa ni, babu wani abu da nake kyama kuma babu wani abu da yake ba ni haushi, duk san da aka ce min fito rekodin toh kawai ji nake kamar Uwata ta kada kishiyarta kawai farin ciki na ke, domin na san za a yi nishadi ne, a yi dariya kawai a dawo. Wallahi kullum cikin jin dadi nake alhamdulillahi in dai a shirin Dadin kowa ne muna godiya ga Jama’ar mu na gidan ma kamar shugaban gidan kamar shi Gumel shugaban gidan ‘Arewa24’ din namu na bangaren mu, akwai kamar su Nura, akwai kamar su daraktocin mu su Mujahid, su Baharu, su Turufa, wallahi duk muna godiya garesusu, saboda suna ba mu kulawa sosai kamar T-Balarabe (Bossy), musamman shi Jajirtacce ne a wannan layin ya kan tsaya kai da kafa wasa a yi dariya, ba dai bacin rai hajjiya. Ko da hawan ini ka je wurin nan sai ya sauka Allah kuwa, kuma in muka hadu kamar kar mu rabu, kowa na son kowa, kullum haka ne ba wani abu da yake daban a wurina kowanne mai dadi ne.

Wanne irin rawa kika fi son takawa a bangaren film?

Idan aka ce miki wannan Jarumi ne kin gane? ana so a sami komai da komai a wurin shi ba shi da wani zabi, menene ba shi da wani zabi? idan aka ce sai ka zaba toh kenan abinda ranka ya ke so za ka zo ka yi, yanzu misali in kiraki in ce ina so ki fito min a me fada ke kuma yana yin ki ba na ma masu fadan bane, toh! sai ki ji abin ya zame miki banbarakwai, toh amma in sana’arki ne yau da gobe, ina ce miki yi fada za ki kama fada kin gane?, idan kuma na ce “Hajjiya Rabi fito min a me hakuri” sai ki fito ‘Silent’ ki fito a me hakuri alhalin ya na yinki ma watakila yana yana yi da masu fada din, ai duk jarumi in ya ce miki ba zai iya abu ba toh ba jarumin gaske bane, ai duk rol din da aka baka kawai ka hau kai ka zauna, shi ne ka ciri tuta Hajjiya ka kai kuma jarumi. Amma idan aka baka rol aka ce yi rol din hakuri “ah! ni ban iya ba ni na fi sin fada” toh! ka zama kare kenan kullum kai kenan cikin haushi? kin ga ba zai yu ba, ai duk rol din da aka ba ni ni dai Zahra’u duk wanda kika kawon zan iyai miki shi kuma zan yi shi kuma zan hau shi, gaskiya shi ne aktin, amma daga ba haka ba ni ban san wani abu bayan haka ba, domin jarumi an sanshi dai da jajircewa.

Da wa kika fi so a hadaki a fim?

Ni duk wanda aka kawo zan yi aiki da shi domin abokin aiki ne, ba ni da wani zabi duk wanda aka hadani da shi jarumine dai yana wasan nan, kai! ko sabon zuwa ne ai kowa koyo ya yi, kawai za mu yi aiki ne ni duk wanda aka hadani da shi, ni dai kawai fatana ubangiji ya budo kofofi kawai na alkhairi, amma duk wanda aka hadani da shi alhamdulillahi ni ba ni da wani wanda nake kyama duka kannywood, rankatakaf! din cikinta da bayanta ba wanda nake kyama kuma ba wanda ya tsare min gaba kuma babu wanda ya tsare mun wani abu, kuma babu wani abu da ya shige min duhu, duk wani jarumi in aka hadani da shi za mu taka rawar mu da shi lafiya mu tashi lafiya saboda ba iya guduna a ‘yan kore ba zan fasa musu ba.

Ko akwai wani fim da kika taba daukar nauyinsa, ko kuwa iya fito wa cikin film kawai ki ke yi matsayin jaruma?

Hajjiya ni ‘yar koyo ce Jaruma ce ni amma ‘yar koyo, ai wanda bai iya ba bai isa ya sa jarinsa a wannan gurin ba, koyo nake yi sai na iya tukunna zan fara ina da niyya amma har yanzu ban iya ba, so nake sai na goge sannan zan shigo da kafa ta.

Za ki ga wasu mutanen na yiwa wasu jaruman wani irin kallo musamman masu fitowa a wata dabi’ar ta daban, kamar mugun hali ko masifa ko kuma rashin jituwa da wani a cikin fim, sai a rinka ganin kamar har a zahirance wannan dabi’ar haka take a wajensu, me za ki ce akan hakan?

Eh! haka ne, za a rinka yiwa mutum wani irin kallo ka fito a matsiyaci, ko a me arziki. Toh! shi dai labari kira ne, akwai rol din da idan ni zan yi shi misali idan ka kiraho wata ba ni din ba, ba za ta iya kawo maka abinda kake so din ba, domin wani abun a fuskarka za a same shi, wani abun kuma a jikinka za a same shi, imoshan dinka ko ri’akshan dinka, eh! labari kira ne, dan haka kallon da suke yi wa mutanen dole ne su yiwa mutanen kallo saboda mutanen ne masana’anta ce mai fadi na fada miki, sannan tana dauki da mutane iri daban-daban, da masu kirkin da marasa kirkin duk ana hade guri daya, toh kinga dan haka dan an maka wani kallo ma dai, amma dai ai an san wasa dai ai wasa ne, za ka je ka yi fim ka mutu a saka a makara aje a binne, gobe a sake ganinka a wani fim din in da ka mutu din, mutuwar gaskiya ce ai da ‘yan fim din ma sun kare ko? Gaskiya ne toh shi ne dai abinda mutane wasu ba su fahimta ba, amma da yawa wasu sun fahimta.

Yanzu misali a cikin yaranki wata ta fito ta ce tana son ta shiga harkar fim, shin za ki amince ki barta ta yi ko kuwa ba ki da ra’ayin hakan?

Eh! Gaskiya ba zan barta ba,dalili kuwa abin ya lalace ba irin na da bane, in kamar irin na da ne wallahi lafiya lau zan barta ta yi, amma a yanzu wallahi ba zan bari ba, sai inda karfina ya kare gaskiya wannan saboda masana’antar ta mu na fada miki tana da fadi kuma mun samu gurbatattu da dama, amma da ‘da’ ne yarana dan sun ce za su yi ‘normal’ zan kai su su yi, amma banda yanzu saboda abin ya zama abin tsoro ya zama abu al’ajabi, kamar mu dattawa dai ba za a nuna mana wasu abubuwa ba, amma kin san dai ba a rasa gurbatattu a kowacce sabga ko?.

Za mu cigaba a mako mai zuwa.

 

Exit mobile version