Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta bayyana cewa, har yanzu ba ta kammala cire tallafin mai ba a cikin kasar.
Karamin ministan Mai, Mista Timipre Sylba, shi ne ya bayyana hakan lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a ranar Litinin. Ministan ya kuma bayyana cewa, gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta fara gyara bangaren mai.
A cewar ministan, “mun yin kokarin cire tallafin mai gaba daya. Amma mun kasa yin hakan, inda har yanzu ba mu cire tallafin mai kashi dari ba daga cikin harajin da muke samu na kasuwancin kasashen ketare.
“Idan muka cire gaba daya muka bar mutane su sayi mai bisa yadda yake a kasuwan duniya, to za a samu karin farashin mai fiye da wanda kuke gani a yanzu.
Wannan kalamai na Sylba ya yi dai-dai da kalamunsa na watan Satumbar shekarar 2020, wanda yake cewa gwamnatin tarayya ta cire kudaden tallafi na naira biliyan 500 daga cikin kasafin kudi. Haka kuma Sylba ya bayyana cewa, gwamnatin tarayya ta bai wa kamfanin mai na kasa farashin na musamman ta yadda tsadar man zai kasance. “dukkan kudaden da muke amfani da su mun dogara ne da naira a wancen lokaci kuma ana biyan tallafin ne da dala wanda a yanzu farashinta ya tashi sama,” in ji shi.
Mun tabbatar da mukarrabanmu da ke Abuja a wancen lokaci cewa, za a cire tallafi domin Nijeriya ta tanadi naira tiriliyan daya. Ya ce, za a yi amfani da wadannan kudade ne domin bunkasa wasu fannikan tattalin arziki.
Binciken da kamfanin mai ya gudanar ya nuna cewa, kalamun minista ne ya harzuka wasu ma’aikatan da ke cikin kungiyar kwadugo ficewa daga zauran taro a ranar Lahadi tare da ministan kwadugo, Dakta Chris Ngige a kan karin wutar lantarki da kuma farashin mai.
“Idan har ana sayar da litan mai a kan naira 170 kuma minister yana da tabbacin da abin da yake fada, to ya zo ya fada wa ‘yan Nijeriya kudin da aka tanada da kuma dalilan da ya sa aka gyara bangaren mai,” in ji shugaban kunfiyar kare maradun ma’aikatan Nijeriya.
Ministan ya bayyana cewa, an gudanar da gyararraki a bangaren kalanzir da gas da dadewa, bai da dalilin da zai sa ba za a gudanar da haka ba a bangaren mai. Lokacin da ministan yake amsa tambaya a kan yanda gwamnatin tarayya ta gudanar da yarjejeniyar shigo da mai daga kasar Nijar ba zai zama wani abun kunya ba, sai ministan ya bayyana cewa, ba zai zama ba
“Ni ban ga wani abun kunya ba a ciki. Nijeriya ta kasance babban kasa wajen gudanar da kasuwancin mai. Dole muna bukatar mai. Ida kuwa dukkan matatun maimu suna aiki yadda ya dace, muna bukatar karin mai.
“Nigar suna da mai kuma kasa ce da ke da kyakkyawan alaka da Nijeriya. Tana da matatun da za su iya tace mana man da muke bukata.
A cikin watan Maris, gwamnatin tarayya ta hannun hukumar kulawa da kayyade farashin mai ta kasa (PPPRA) ta samar da kayyade farashin mai bisa la’akari da yadda kasuwa ta kaya. Sakamakon wannan umurni, a wannan mako mai a wurin sari ya kai naira 138.62 wanda ake sayar da kowani lita daya a kan naira 151.56.
“Yanzu lokaci ne da ‘yan Nijeriya suke fuskantar zahirin abin da ya kamata. An gudanar da wannan gyara ne a bangaren mai domin a samu kudade masu yawa. A kalla kowata shekara muna iya tanadar miliyoyin kudade masu yawa.
“Tuni muka cire tallafi a cikin kasafin kudi na naira biliyan 500. Haka kuma mun bai wa kamfanin NNPC farashin na musamman ta yadda tsadar farashin zai kasance. Dukkan kudaden da muke amfani da su a kan naira ne kuma ana biyan tallafin mai ne da dala, inda a yanzu dalar ta tashi sosai,” in ji Sylba