Jam’iyyar PDP ta nunar da cewa har yanzu fa tsugune ba ta kare ba dangane da zargin aringizon kasafin kudin 2024 da Sanata Abduk Ningi ya kwarmata. Inda ta yi kira ga Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sake yin nazari da kuma gudanar da kwakkwaran bincike na gaggawa dangane da kasafin kudin.
Sakataren yada labarai na jam’iyyar na kasa, Debo Ologunagba, ya fitar, da wata sanarwa da ta bayyana cewa PDP tana nan kan bakanta na ganin shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya gurfana a hukumar yaki da cin hanci da rashawa domin a bincike shi kan yadda naira biliyan 108 na Jihar Akwa Ibom suka bace da kuma naira biliyan 86 da aka bayar da kwangila ba bisa ka’ida ba a lokacin yana gwamna da kuma ministan kula da bunkasa yankin Neja Delta.
- Ɗiawara Ya Fice Daga Tawagar Faransa Bayan An Hana ‘Yan Wasa Yin Azumi
- An Fara Taron Kasa Da Kasa Kan Tsarin Dimokuradiyya Karo Na Uku A Nan Birnin Beijing
Haka kuma jam’iyyar ta caccaki Sanata Akpabio da shugabannin APC kan kawar da hankalin mutane na rashin gudanar da bincike a fili na zaargin cusa naira tiriliyan 3.7 da aka yi a cikin kasafin kudin 2024.
“Jam’iyyar PDP ta tabbatar da cewa idan aka tsana bincike za a gano asalin gaskiya game da arangizo a kasafin kudin 2024 da kuma adadin yawan kudaden da aka raba wa ‘yan majalisa na APC,” in ji sanarwar.
Ta kara da cewa wannan lamarin da ya faru ya tabbatar da cewa akwai masu hana ruwa gudu a cikin APC wajen gudanar da shugabancin Akpabio a zauren majalisa wadannda ba su damu da halin da talakawan Nijeriya ke ciki ba.
“Abin bakin ciki ne a irin wannan yanayin da Nijeriya ke fama da matsin tattalin arziki a ce shugabannin APC a zauren majalisa suna kin bayyana gaskiya kan zargin almundahanan kan kuaden da za a kawo wa ‘yan Nijeriya sauki a rayuwarsu.”
PDP ta ce Akpabio da ke shugabantar APC a zauren majalisa babu wata barazana ko dakatarwa da zai hana ‘yan adawa fallasa arangizon kudaden al’umma ta hanyar fitar da sanarwa, rubuce-rubuce a kafaken yada labarai wajen ganin an gudanar da bincike kan zargin yin cushe a kasafin kudi.
Sanarwar ta bayyana cewa jam’iyyar PDP da ‘yan Nijeriya ba sa shakkan shugabannin APC a zauren majalisa, domin wannan cin hanci ne karara a bayyanar jama’a, amma ake kokarin yin rufa-rufa.
Ta ce rashin gudanar da bincike kan zargin cushe a kasafin kudin zai taba kimar majalisar kasa da kuma lalata ayyukan ‘yan majalisa da tsarin mulki da dora musu na gudanar da bincike kan yadda ake kashe kudaden al’umma, sannan kuma ya taba kimar dimokuradiyyar kasar nan idan har aka kasa gudanar da binciken gaggawa.
A cewar PDP, idan har Sanata Akpabio zai yi adalci, to ya gaggauta janye dakatarwar da aka yi wa Sanata Abdul Ningi tare da barin a gudanar da bincike kan arangizon naira tiriliyan 3.7 a cikin kasafin kudin 2024.
Sanarwar ta ce, “Jam’iyyarmu tana aiki kafada da kafada da ‘yan Nijeriya kuma ba za su janye ba har sai Sanata Akpabio ya bari an gudanar da sahihin bincike kan wannan labari da ya zartar da hukunci bisa kuskure.”