Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa kawo ƙarshen ta’addanci da hare-haren ‘yan bindiga yana daga cikin manyan abubuwan da gwamnatinsa ta fi mayar da hankali a kai.
Shugaban, ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin ƙaddamar da sabbin gidajen zama ga mutanen da hare-haren ‘yan bindiga ya shafa a Jihar Kaduna.
Tinubu, wanda mai ba shi shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya wakilta, ya ce: “Yaƙi da ta’addanci babban ƙalubale ne, amma kawo ƙarshensa babban abu ne a cikin ajandar tsaron ƙasa. Nijeriya tana hannun ƙwararru kuma za mu dawo da doka da oda.”
Wannan aikin gine-ginen an yi shi ne tare da haɗin gwiwar Qatar Charity Organisation, a matsayin wani ɓangare na shirin gwamnatin tarayya na farfaɗo da al’ummar da rikice-rikice suka shafa.
Tinubu ya ce an samu ci gaba sosai wajen dawo da zaman lafiya da taimaka wa mutane su farfaɗo da rayuwarsu a Jihar Kaduna.
“Farfaɗowa na samuwa, kuma a bayyane yake cewa sabon yanayi na sauyi yana faruwa a Kaduna,” in ji shi.
Ya jaddada cewa kyakkyawar gwamnati na nufin kula da buƙatun al’umma, musamman waɗanda rikici ya shafa.
“Muna share hawayen waɗanda rikice-rikice suka shafa. Muna haɗa kan al’umma. Muna tabbatar da cewa kowa yana da wajen zama da jin cewa yana da muhimmanci,” in ji Tinubu.
Shugaban ya yaba wa gwamnatin Jihar Kaduna, ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, da kuma hafsan hafsoshin tsaro bisa matakan soja da na lumana da suke ɗauka don shawo kan matsalar tsaro.
“Zaman lafiya na gaskiya sai an gina shi, ba zai zo da ƙarfi ko tsoratarwa ba,” in ji shi.
Ya ce buɗe kasuwar Birnin Gwari da komawar manoma zuwa gonakinsu alama ce ta ci gaba.
“Wannan alama ce cewa Kaduna tana fuskantar sabon salo, salo na gaskiya da gyara,” ya ƙara da cewa.
Yayin da yake magana da waɗanda rikicin ya shafa, Tinubu ya ce: “Kun fuskanci tashin hankali, amma muna tare da ku. Gwamnatinku na ganinku kuma tana jin zafin da kuke ciki.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp