An Harbe Shi Da Bindiga A Rukunin Gidajen ‘Yan Majalisun Tarayya

– Jami’an Tsaro Sun Ji Tsoron Yin Bincike – Aminu

Daga Abdulrazaq Yahuza Jere, Abuja

Wani matashi, Aminu Ibrahim da ke zaune a yanki na biyar (Zone E) a rukunin Gidajen ‘Yan Majalisun Tarayya da ke Unguwar Apo a cikin garin Abuja, ya tsallaka rijiya da baya bayan wani harsashin bindiga da aka harbo ya goge shi a kafada dab da wuyarsa.

Mazauna yankin sun razana da harbin bindigar da aka yi a cikin yankin nasu a ranar Asabar da ta gabata, kasancewar har zuwa lokacin da ake rubuta wannan rahoton ba a gano katamaimen wuri ko wanda ya yi harbin ba.

A cewar Aminu wanda bai wuce shekara 26 ba a duniya, al’amarin ya faru da misalin karfe 8:30 na safe a yayin da ya fito don wanke baki domin shirin Karin kumallo.

Ya bayyana wa LEADERSHIP A Yau yadda al’amarin ya faru.

“Na fito ina brush (goge baki) da safe su kuma wasu ‘yan’uwana su biyu suna wanki a gefe muna hira. Ina cikin brush sai buroshin ya kufce ya faxi kasa, garin in sunkuya in dauka sai na ji kamar wani dutse ne ya sukuto mun. Na ji wani zafi a jikina, sai na ji idona yana jujjuyawa ina jin jiri. ‘Yan’uwan nawa sai suke tambaya na “me ya faru?” saboda sun ji kara. Kawai cikin minti daya ko minti biyu ina cikin komawa daki ban san me yake faruwa ba, kafin in Ankara sai nag a bullet (harsashi) a kasa. Sai na tambayi ‘yan’uwan nawa me ya faru ne? Suka ce ai harbi (na bindiga) suka ji amma ba su san daga ina ne aka yi harbin ba amma da yake Allah ya takaita harbin bai same ni da kyau ba; ya goge ni ne a kafada kusa da wuyana, ban ma san na ji ciwo ba. Daga baya sai na ji wajen na mun zafi, da na je cire rigana sai na ga ashe duk jini ya bata rigar. Mun bar bullet (harsashin) da aka harbo a wurin muka ce kar kowa ya dauka domin ba aikinmu ba ne, aikin hukuma ne su zo su dauki bullet din kuma su gano daga ina ne aka yi harbin”.

Aminu, ya kuma bayyana yadda suka kai rahoton faruwar lamarin ga ofishin ‘yansanda mafi kusa da su da kuma irin abin da ya biyo baya.

“Mun kai report (rahoto) a police station (ofishin ‘yansanda) na Zone A, Apo Distric (Shiyya ta daya a Gundumar Apo), da kyar dai suka yarda suka ba mu dansanda guda daya, ya zo shi ma ya yi dube-dubenshi; shi ma ya kasa gano daga inda aka yi harbin… sai ya dauki bullet din ya kai satation (ofishinsu). Su ma (a nan ofishin na su) sun kasa gano abin, wasu su ce bullet ne na pistol (karamar bindiga) wasu kuma su ce na AK ne (madaidaiciyar bindiga) kuma ba su bamu shawara yadda ya kamata ba, illa suka ce mu je mu yi ta addu’a kuma mu sa ido dangane da abin da yake faruwa a wajen”.

Aminu ya yi zargin cewa saboda abin ba ya faru ne da manya ba watakila shi ya sa aka yi sako-sako da daukan kwakkwaran mataki a kai wanda a cewarsa wannan ba karamar illa ba ce ga zamantakewar kasar.

“A kasar nan, in dai kai ba wani ba ne kuma ba ka san wani a cikin man ya ba, duk abin da ya same ka sai dai ya bi iska. Mun kira wani muka fada masa sai ya ce ai bai kamata mu bar lamarin kawai haka ba, domin duk wanda yake rayuwa a wurin rayuwarsa tana cikin hadari”.

A Aminu, wannan mutumin da suka shaida masa halin da ake ciki, ya tura su zuwa ofishin sashen da ke kula da yaki da ‘yanfashi na ‘yansanda (SARS), sai dai su ma da alama abin ya fi karfinsu.

“Mun je ofishin SARS na cikin garin Abuja suka ba mu officers (jami’an tsaro) guda biyar muka zo wajen da su, dama kafin mu taho da su akwai gida da muke suspecting (zargi) don wurin kamar jeji ne sai wani estate (rukunin gidaje), muna zargin idan ma harbi za a yi to ba zai wuce daga wajen ba, saboda su gidan ba su da aikin yi sai jin kida da kuma shaye-shaye. Sannan idan sun yi shaye-shayen a cikin gidanmu suke zubar da kwalabensu na shaye-shayen da wasu abubuwan maye. To, da muka zo da ‘Yan SARS guda biyar suka auna da kwarewarsu su ma suka ce ai daga nan gidan aka yi harbin”.

Da aka tambaye shi halin da ake ciki tun da jami’an tsaro sun shigo cikin lamarin, Aminu ya bayyana cewa bai gamsu ba da yadda suka dauki lamarin ba.

“Matsayin da ake ciki ni ban gamsu da shi ba… sun ce nan Abuja ne; suna tsoron kar su auka ciki a ce musu ai gidan wani Minista ne ko ‘ya’yan Minista ne; daga karshe ma abin ya zo ya shafi aikinsu. Suka ce mu yi kokari mu gano sunan maigidan da gidan, in an gano; su kuma daga nan office za su rubuto search warrant (takardar izinin bincike) su zo gidan su yi bincike. Amma ba zai yiwu su zo haka kawai su shiga gidan ba ba tare da wani kwakkwaran evidence (shaida) ba. Gidan a Lavana Court Zone E yake”. A zargin da ya yi.

Da aka tambaye shi ko akwai wasu da ba sa ga-maciji da su a cikin yankin? Aminu ya ce, “a’a, ba na tunanin hakan, domin ba na harka da mutanen banza kuma ba wai ina wani business (harkalla) ba ne ballatana a ce za a yi mun hakan, kuma ni ba na neman mata balle a ce na je na nemi budurwar wani ne yake jin haushi na, hasali ma ni ban da budurwa. Sannan abin da ya faru ba kuskuren harbi ba ne, target (nufin harbi) din an yi ne a harbe ni a kai! Allah ne kawai ya yi akwai brush a hannuna ya fadi, na sunkuya zan dauka sai aka yi loosing target (rashin sa’ar samu)”.

Da yake tsokaci kam lamarin, daya daga cikin mazauna yankin, Limamin Masallacin Zone E na rukunin Gidajen ‘yanmajalisun tarayya, Ustaz Ibrahim Lawal Usamah, ya ce ba yau aka saba ganin haka ba a yankin, amma na wannan karon ya tayar masu da hankali.

“Ai wannan abin bai ba mu mamaki ba, saboda mafi yawanci a nan irin hakan ta faru. An hallaka masu Keke Napep a wurin… daga baya aka ba da rahoton cewa ‘yan boko haram ne mu kuma muka kira ‘yanjarida muka ce ba gaskiya ba ne. Daga karshe kotu ta tabbatar da cewa ba ‘yan boko haram ba ne har ta ba da damar a biya diyya… Wannan abin da ya faru, an kawo ma’aikata su yi aikinsu amma suna jin tsoron kar su shiga abin ya shafi aikinsu saboda suna tunanin ko gidan Minista ne, ka ga a irin wannan kasar sai a ce ‘wa iyazu billahi’, tunda a ce ma’aikaci zai iya yin aiki ne a kan talaka amma ba zai iya a kan wani babba ba. Idan har ya zama akwai wanda ya fi karfin doka a kasar nan; to ba za a taba samun gyara ba,” in ji shi.

Ya ce wanda abin ya faru da shi, Aminu matashi ne dan bautar kasa da ake bukata a kasar nan, don haka rasa shi zai iya haifar da matsala, sannan ya ce “dole abin ya tada mana da hankali, domin matashi ne shi ba kamar irin mu ba da za mu ce mun dade a duniya,” kamar yadda Ustaz Usamah ya bayyana.

Da LEADERSHIP A Yau ta tuntubi ofishin ‘yansanda na shiyya ta daya (Zone A) da ke cikin rukunin gidajen ‘yanmajalisun wanda aka fara kai wa karar abin, sun tabbatar da samun rahoton aukuwar lamarin, sai dai sun ce babu wani Karin bayani da za su yi kasancewar jami’in da aka same shi a bakin aiki maisuna Ezekiel Akhigbe ya ce wanda ya karbi rahoton lamarin ba ya nan.

 

Exit mobile version