Connect with us

TATTAUNAWA

Buhari Ya Yi Kokari A Harkar Tsaro, Amma —Husaini Gambo (2)

Published

on

Ci gaba daga makon jiya na tattaunawar da Wakilinmu na Yola ya yi da shugaban kungiyar Adamawa ‘Concent Citizen Foundation’ kuma mai akidar Buhari a zaben 2015, Husaini Gambo wanda ya nuna bayar da kai bori ya hau da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kan rikita-rikitar jam’iyyar APC da cewa, abin kunya ne. Sannan ya tabo batun almundahana da kwamitin Justis Bobbo Umar ya bankado kan tsohuwar gwamnatin Murtala Nyako. A sha karatu Lafiya:

 

Idan muka dawo nan jihar Admawa, ku ma jam’iyya dai ita ce jagorar tafiya, kuma sai ga shi bisa ga alamu ta fada hannun su tsohon gwamna Murtala Nyako. Ina makomarku?

Ta ina za ta koma? Ai idan mutum ya ce zai ba ka riga, Hausawa sukan ce ka duba ta wuyansa. Ba yadda za a yi gwamna mai ci a kwace jam’iyya a hannunsa a ba wanda ba gwamna mai ci ba. Gwamnan nan fa shi yake da kananan hukumomi 21, shi yake da kansiloli, shi yake da kwamishinoni, shi da kansa yake karba, ba yadda za a yi shugaban kasa ya hana ‘Allocation’ na Adamawa ya shigo Adamawa.

Lokacin da ake fada da Nyako aka ce an kwace jam’iyyar PDP a hannun Nyako, lokacin ne dukkanmu muka koma jam’iyyar APC, yau APC ta yi tasiri ko ba ta yi ba? Ina PDP take? In aka ce za a kwace jam’iyyar APC a hannun gwamna mai ci, a ba wani, sai ya tafi shi kuma ya zuba musu ido, in ya ga dama ya canja jam’iyyar, domin dokar kasa ta ba shi dama, in akwai baraka ya iya canja jam’iyya. To amma ba za a iya yin wannan ba, domin muna son a bambance tsakanin gaskiya da karya, a bambance tsakanin duma da kabewa, in ba haka ba wa ya isa ya ce maka zai kwace jam’iyya a hannun Bindow, ya ba wa?

 

Kai mene ne ra’ayinka, zabe kake son a yi ko ya ya?

Ni abin da nake bukata, Hausawa sukan ce ‘da sabon gini gara yabe.’ Ka ga tsofaffin ‘Edecutibes’ dalilinsu ne muka samo wadanda suka zama mutanen kirki. Saboda haka me suka yi mana? ‘Edecutibe’ na fati ba zai hana ka ba, ba zai ba ka ba. Amma mutumin da za ka sa shi ya je ya zabo maka mutane nagari, shi ne abin dubawa. Yanzu idan ka duba wadanda suka fito da sababbin ‘yan takaka din nan ka sa su a Faifai ka tantance su, ba su zo da manufa mai kyau ga jam’iyyar APC ba. Shi ya sa su Tinibu suke bukatar su karbi mulki a wajen Buhari cikin sauki, da kansa ya lalata jam’iyyar, su kuma su gyarata.

Saboda haka mu ba za mu canja wadanda suke kan kujera ba, sai dai muna son su duba wadanda suka cancanta. Yanzu a Adamawa Bindow shi ne na farko, kamar a Sanata, Adamawa central ba mu da kowa za mu canja, za mu kawo wanda jama’a suka ce suna so, shi ne Bello Hamman Daram, yana da kwarewa da nuna hazaka, ga shi da kishin ci gaba.

Haka kuma mamba na kananan hukumomin Girei, Yola North, Yola South, Barista Lawan Garba ba ya bada kudi, amma yana samar wa yara abin dogaro da kai na shekara talatin, dole ne irin wadannan su dawo saboda ayyukan da yake yi. Domin shi ba Kifi yake bayarwa ba, yadda za ka kama Kifin yake yi wa yaran talakawa, irinsa muke so.

Kamar shi Suleiman, mamba dinmu, shi ma ya yi aiki yana bada jari ga yara yadda za su dogara da kansu. Saboda haka mu a nan Jimeta (Yola North) ba mu da wata damuwa illa kawai muna jiran Allah ya nuna mana lokacin zabe. Amma wai maganar wani ya zo ya kwace jam’iyya bai ta so ba.

 

Kwanan baya kwamitin Justis Bobboi Umar ya fitar da sakamakon bincike kan tsohowar gwamna Nyako. Me ye ra’ayinka?

Ni na je gaban Justis Bobbo Umar kafin Allah ya yi masa rasuwa, ya ce min ko a lahiri zai bada shaida akanta. Ya ce an ba shi toshiyar Naira miliyan dari biyu a kan cewa kada ya yi wannan commission, in zai yi kuma ya taimaka, ya ce ba zai yi ba, shi adalci zai yi tsakaninsa da Allah, ba ya bukatar ko kwabo. Ya gaya min cewa Lauyan da aka dauka an ba shi Naira miyan saba’in, Lauyan ya zo ya same shi har gida a kan don Allah ya taimaka, ya ce shi ba zai taimaka ba, zai yi abin da ya dace domin yana tuna mutuwarsa, kuma sai ga shi Allah ya dauki ransa.

Saboda haka irin almundahanan da sakamakon binciken ya samar, ai ya wuce kima, an ce fa an bada kudi daga 2007-2014, an karbi rarar kudi Naira miliyan dubu dari biyar da arba’in da uku da miliyan dari takwas da ashirin da takwas da dubu dari da daya da ashirin da tara da kwabo hamsin da tara (N543, 828, 870, 129.59). Wadannan su ne kudaden da kwamitin ya gano gwamnatin ya karba a shekara bakwai, amma a ciki akwai inda tsakanin ofishin Accouter General da Kwamishinan kudi a kawo yadda lissafi zai hadu, ya gagara.

An samu rarar Naira miliyan dubu tamanin da daya da miliyan dari takwas da tamanin da shida, abin takaici aka ce daga 24/12/2012 zuwa 7/12/2013, an cire Naira miliyan dubu tara da miliyan dari takwas da tamanin da Shida (N9, 886, 000,000:00).  Akwai kudin taimaka wa shan man jami’an tsaro, don Allah motoci nawa ne ake sa wa mai? Kuma batun wutar kan titi (Street light) tsakanin cikin Jimeta-Yola da Mubi an cire zunzurutun kudin waya ba karafunan da za a saka ba, kudin waya kawai Naira miliyan dubu goma.

Amma a lokacin tsohon gwamna Nyako an samu kyaututuwar yanayin tsaro da ya hana ‘yan Boko Haram su shigo Adamawa.

A’a, wanda ya taimaka aka samu tsaro mai kyau shi ne Bala Nggilari, da Bala Nggilari ba ya kan mulki da mun dade da barin Adamawa. Bala shi ne ya yaki Boko Haram tsakaninsa da Allah, ya bar maganar su Goodluck a matsayinsa na dan Adamawa ya tsaya ya kare mutanensa, ai wadancan kam suna sama da fadi ne. A tsaro ne aka kusa harbe gwamnan a Michika ko ka manta?

Saboda haka da Nyako ke kan kujera ake gudu, yana nan ake kashe-kashe ba baya nan ba, yana nan mutane daga Madagali sun dawo Michika, daga Michika sun gudu sun koma Mubi, daga Mubi sun gudu sun koma Maiha, sun dawo Hong-Gombi, daga nan kuma sun gudu sun dawo Song, daga nan din ma ‘yan Boko Haram suna cewa ai Yola za ku tafi, ku je Yolan muna zuwa. To ina tsaron yake?

 

Yanzu me kuke son ganin gwamnatin jihar ta yi game da wannan rahoton?

A’a, dama shi Bindow ba mai fada ba ne, ba mafadaci ba ne, da Bindow mafadaci ne wani ba zai fita gidan Radiyo ya ce masa azzulumi ba, akwai wadanda muka sansu daga cikin wadancan mutane, yanzu ka ketare gadar nan, inda Toliget yake, filin na waye? Na shugaban jam’iyya, ina ya samu? Da ya ya ya shigo jam’iyyar, mutumin da ko daki ba shi da shi, ya shigo jam’iyya.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: