Connect with us

Bakon Marubuci

Harkar ilimi Ta Taka Kaya A Gonar Korona?

Published

on

Yau kimanin watanni hudu kenan da kasancewar daukwacin makarantu a Nijeriya kulle, wanda hakan ya zo ne ta dalilin bin hanyoyi tare da matakan yaki da yaduwar annobar korona, lamarin da ya rutsa har da  tunanin daukar matakin da wahala ya bari a rubuta jarrabawar karshe (SSCE), wadda daliban sakandire ke zana wa kowace shekara. To amma kuma duk da hakan, idan an bi ta barawo, a bi ta mabi sawu mana, a sake duba batun, ta hanyar yin nazarin bin wata hanya.

Masu fasahar zance sun ce: idan hagu ta kiya, a koma dama mana. Duk da yadda yake, hakki ne a kiyaye rayuwakan yan kasa tare da daukar dukan matakin da ya dace wajen hana yaduwar wannan hattsabibiyar annobar korona, shima nauyi ne babba wajen bai wa yan kasa ilimi, don ci gaba kuma ya na da kyau gwamnatoci su sake sabon lale, wajen nemo wata hanyar da za a bayar dashi ko sake nazarin bude makarantun a cikin yanayin taka-tsan-tsan da kwararan matakai.

Sanin kowa ne kan cewa, sakamakon yaduwar annobar korona a kasashen duniya, al’amarin da ya jawo cutar ta shafi kowane bangaren rayuwar yau da kullum na al’ummar duniya, wanda ya hada da tattalin arziki, kiwon lafiya, tsarin ilimi da zamantakewa, daga ciki har da tarayyar Nijeriya da takwarorin ta a Afrika, inda hakan ya tikasta kasashen duniya daukar matakan kariya tare da yaki da bazuwar annobar a ciki da waje.

Dangane da hakan ya jawo gwamnatocin kasashen duniya daukar ingantattun matakan shawo kan yaduwar annobar, ta hanyar gindaya sharudda da ka’idojin da za a bi wajen kare kai tare da dakile yaduwar cutar. Wadanda su ka hada da takaita zirga-zirga tsakanin jihohi, kulle wasu manyan garuruwa tare da samar da cibiyoyin ko-ta- kwana don killace wadanda su ka hatbu da ita.

Bisa ga hakan, ranar 19 Maris ma’aikatar ilimi ta tarayyar Nijeriya ta shelanta daukar matakan kulle ilahirin makarantu a kasar baki daya- wanda ya fara aiki ranar 23 ga watan na Maris, daga cikin matakan dakile bazuwar annobar korona.

Biyo bayan daukar wannan matakin, masana tare da masu lura da al’amurra sun dora tambayoyi da dama dangane da hakan: wanda ya hada da son sanin- shin akwai hanyar sadarwar zamani a Nijeriya da zai maye gurbin kuma ya biya bukatar dalibai sama da miliyan 46 wadanda matakin ya shafa- wajen samun ilimi? Sannan shin iyaye sun tanadi kayan da za su yi amfani da su wajen koyar da yayan su- bayan matakin? Kuma shin mu na da kwararrun malaman da za su iya tsarawa da bayar da kwasa-kwasai ta hanyar kafofin sadarwa na zamani (MOOC)?

Bugu da kari kuma, idan ba a manta ba, a baya Nijeriya ta yi kaurin suna a fannin yawan adadin yaran da ba su zuwa makarantu, wanda mu ke da adadin yara kanana kimanin miliyan 13.2 da basu zuwa makaranta, a matsayin kaso mafi yawa a fadin duniya. Wanda duk da yadda yake a doka, dole kowane yaro ya samu ilimin farko; shekaru tara (9) na farko a rayuwar sa, amma hakan ya gagara ta dalilai da dama- wadanda su ka hada da talauci, al’ada, fahimtun wasu masu addini, ko yanayin wasu bangare da makamantan su.

Har wala yau kuma, da matsalar ko-in-kula da wani lokaci ake samu a bangaren gwamnatoci, wanda a kasafin kudin Nijeriya na 2020 ta ware kashi bakwai kacal (7%) cikin dari a fannin ilimi, sabanin yadda ya dace; kaso15 zuwa 20 da hukumar UNESCO ta tsara.

Haka zalika kuma, Allah kadai ya san gibin da wannan matakin ya kawo a sha’anin ilimi, kuma wani babban abin fargaba shi ne, shin yaushe za a kawo karshen kullen makarantu a Nijeriya? Kuma wane hali wadannan daliban su ke, su na ci gaba da bibiyar darussan su ko kaka? Wanda kuma har yanzu babu tabbacin samun wani takamaiman tallafin da zai karfafi gwiwar wadannan daliban a sha’anin ilimin su.

Sannan lura da sabon tsarin da manyan kasashen duniya da makarantu masu zaman kansu su ka samar, na karatu a budaddiyar jami’a. Sabanin dalibai a Nijeriya, inda mafi yawan su suna karatu a makarantun gwamnati wadanda makamancin wancan tsarin bai kankama ba.

Wanda idan an yi la’akari da hakan, wane hali daliban mu za su kasance? Duk da wasu gwamnatocin jihohi sun kaddamar da tsarin karatu ta hanyar gidajen radiyo da talabijin, wanda idan mun yi sanya tabaraun hangen nesa, kimanin kaso 70 cikin dari na jihohi a Nijeriya ba su iya gamsar da bukatr daliban- yayin da kuma hakan babban koma baya ne a fannin ci gaban ilimi.

A hannu guda, wannan sabon tsarin ba zai kai gaci ba, saboda yadda matsalar wutar lantarki ke ci gaba da samun gindin zama a Nijeriya, ka ga ko da wuya a aiki bawa a garin su ya dawo. Kuma kai ma ka tambayi kanka, akwai wutar lantarki a gidajen mu da har za mu samu zarafin kallon akwatunan talabijin? Wanda hakan yar manuniya ce a sakamakon wani binciken da ya nuna akalla kaso 44 cikin dari na yan Nijeriya su na rayuwa ne a matsanancin talauci, in ji hukumar ‘National Bureau of Statistics’ (NBS) ta Nijeriya.

Saboda haka, ya zama wajibi gwamnati ta dubi wannan batu tare da daukar ingantattun matakan ceto tsarin ilimin kasar nan. Ta hanyar la’akari da hanyoyi da matakan da wasu kasashe su ke bi a yanayi irin wannan. Domin yadda kare rayukan yan kasa yake wajibi, haka samar musu da ilimi yake wajibi. A hannu guda kuma, mutuwa da jahilci yaya da kane suke.
Advertisement

labarai