Shugaban kungiyar masu gidajen gudanar da harkokin kallon wasan Damben gargajiya ta kasa a Nijeriya, Alhaji Aminu Goje Kuceri ta karamar hukumar Tsafe da ke Ihar Zamfara mazaunin unguwar Alabar Rago da ke cikin garin Legas kuma shugaban gidan wasan Damben unguwar Alabar Rago da Akinyale Ibadan da Ilesha baki daya ya ce a halin da ake ciki yanzu ana iya cewa harkokin wasan Damben gargajiya a Nijeriya yana kara samun cigaba tare da daukaka a kasar nan da kewayanta gaba daya.
Aminu Goje Kuceri Wanda ya furta hakan jim kadan bayan tashi daga kallan wasan Damben gargajiya da ke gudana agidan kallan wasan Damben sa dake unguwar Alabar Rago a lokacin da yake zantawa da Jaridar LEADASHIP Hausa a Legas abisa Kan al amuran da suka shafi harkokin wasan Damben gargajiya dake gudana aLegas da kasar nan baki daya ya cigaba da cewar hakika asakamakon irin wannan gag garumin cigaba da harkokin wasannin Damben gargajiya yake samu a Legas da kasa baki daya kungiyar su ta masu gidajen kallan wasan Damben gargajiya ta kasa take tayin kokari har sai taga an sanya wasan Damben gargajiya a cikin tsarin sauran wadansu wasannin gargajiya dake gudana a wadansu kasashen Turawa Wanda al’umma suke kallo a waddnsu kafofin yada labarai na gidajen Talbijin dama wadansu gidajen jaridun Nijeriya baki daya
Haka zalika ya cigaba da cewa a kan haka yake ganin ya kamata ya shawarci sauran masu gidajen kalln wasan Damben gargajiya na Nijeriya su cigaba da sanya gasar kudade ko motoci ga ‘yan wasan Damben gidajen su domin kara bunkasa harkokin wasan da kuma burge masu sha’awar kallon wasan Dambe tare da zaburar da ‘yan wasan a wajen tsayuwa tsayin daka domin burge ‘yan kallon da sauran makaman tansu.
Bugu da Kari yace akan haka yake karayin kiraga masuyin sana,ar Damben gargajiya na kasarnan yace musamman masu ra,ayin shan kwaya ko wiwi da sauran kayan maye kafin shigar su filin wasa ya ce dasu kauce ma yin hakan domin kuwa kungiya ta sanya doka mai tsanani ga dukkan dan wasan da aka samu yana aikata hakan domin kare mutuncin sa da kare mutuncin sana,ar sa ta wasan Damben gargajiya baki daya a karshe ya cigaba da yi wa kungiyar sa ta masu gidajen gudanar da harkokin wasan Damben gargajiya a karkashin jagorancinsa fatan alheri a game da nasarorin da yake samun ab isa jagorancin kungiyar a Nijeriya.