Khalid Idris Doya" />

Hassana Jummai Adamu: Daya Daga Cikin Jaruman Matan Da Suka Bunkasa Ilimi A Neja

Hajiya Hassana Jummai ita ce ke da sarautar YUN WUREN Bargu, tsohuwar malama ce, kuma ta gaji sarauta, sannan a gefe guda kuma fitacciyar ‘yar siyasa. Ta taba zama mataimakiyar shugabar karamar hukumar Bargu, kana ta rike mukamin kwamishiyar mata da ci gaban nakasassu na jiha Minna. Yanzu haka ita ce babbar Darakta mai kula da shirin gwamnatin jihar akan tallafi da ayyuka (GEED).
Wace ce Hajiya Hassana Jummai Adamu?
Hajiya Hassana Jummai Adamu (Yun Wuren Bargu) ita ce jarumar mace ta farko da aka baiwa wannan sarauta saboda kwazonta da jaruntar ta a fagen taimakon al’umma.
An haifeta a Gbere (Wawa) da ke a karamar hukumar Bargu ta jihar Neja. An haife ta ranar 24 ga watan Juli na shekarar 1960, ta fara karatun firamarenta a makarantar firamare ta NEPA a shekarar 1968 zuwa 1973, ta tafi sakandare da ke Okuta na Baptist a 1973-1977. Bayan da ta kammala ta zarce zuwa jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya inda ta samo Diploma akan ilimi da lissafi a 1979-1981, bayan wani dan lokaci kuma YUN WURE ta sake komawa jami’ar Ahmadu Bello din dai don sake neman wata shaidar karatu a shekarar 1984-1987 inda ta fito da darajar digiri akan lissafi (B.Sc (Ed).
Ta dawo fagen aiki, a nan kwalejin gwamnatin tarayya a matsayin jami’ar ilimi ta hudu a shekarar 1989. Bayan wani dan lokaci ta sake komawa jami’ar Abubakar Tafawa Balewa a shekarar 2000-2001 domin karin wani ilimin nata..
A shekarar 2007 ta zamo mai rikon matsayin mataimakiyar shugaban karamar hukumar Bargu, bayan kammala aikin shugabancin karamar hukuma ta koma bakin aikinta inda aka maido da ita kwalejin gwamnatin tarayya da ke Minna a matsayin babbar jami’ar ilimi na kwalejin, inda ta ajiye aiki a shekarar 2008.
A jiye aikinta ke da wuya saboda jarunta da nagartarta a fagen taimakon al’umma ta samu matsayin babbar mataimakiyar gwamna akan ilimin ‘ya’ya mata daga shekarar 2008-2009. Likkafarta ya cilla can gaba inda aka canja mata matsayi zuwa mamba na din-din-din ta uku a hukumar kula da ilimi UBE a shekarar 2009-2011.
Karin shahararta:
Bayan kammala zabe zagaye na biyu a shekarar 2011, ta samu matsayin kwamishiniyar ma’aikatar mata da jin dadin nakasassu, daga shekarar 2011-2015. Hajiya kuma Honorable Hassana Jummai ba ta yi kasa a guiwa ba; ta nemi takarar kujerar majalisar dokokin jihar Neja inda ta samu nasarar cin zaben fidda gwani a lokacin.
Yanzu haka ita ce babbar Darakta mai kula da shirin gwamnatin jiha akan tallafi da ayyuka (GEED), ta taka rawa sosai wajen kawo ci gaba a wannan shirin, inda ta zama abun alfahari ga gwamnan da ya bata wannan aiki.
Kwazonta da jajircewarta ya ba ta damar kasancewa mamba a kwamitin kula da ma’aikatan kwalejin gwamnatin tarayya da ke Kano (FGC) a shekarar 1992-1994. Ta kuma taba zama babbar malama mai kula da wajajen kwanan dalibai a 1994-2011 a FGC da ke Kano. Mamba a kwamitin tsarin jarabawar dalibai ta FGC Minna, a 1997-2000. Ta taba shugabar malamai a makarantar ma’aikatan FGC da ke Minna 1998-2002.
Bayan dawowarta fagen siyasa kuma ta zama shugabar kungiyar ci gaban matan kasar Bargu 2004-2011, tana rike da mukamin ma’ajin hadakar kungiyar KAHAS daga 2005 zuwa yau.
Ta zama mataimakiyar shugaban karamar hukuma na rikon kwarya, inda ta zama mai kula da bangaren ilimi na karamar hukumar 2007-2008. Ta taba zama mamba na kwamitin kudi da ayyukan musamman na karamar hukumar duk dai a 2007-2008.
Kasancewarta fitacciya ya kai ta ga zama shugabar kwamitin kula da makarantu a hukumar UBE ta jihar Neja a 2009-2011, ta kuma zama mamba a kwamitin tsare-tsare na hukumar UBE din a 2009 din zuwa 2011. A shekarar 2011 zuwa 2015 ta zama mamba a hukumar lafiya na matakin farko a jihar Neja, a dai wannan lokacin ta zama mamba a kwamitin kula da allurar Polio, kuma mamba ce a kwamitin tsare-tsare na jiha, a 2012-2015 ta zama mamba a hukumar kula da muhalli ta jiha. Daga 2011-2015 ita mamba ce a majalisar zartaswa ta jiha, a 2014 kuma ta zama mamba a kwamitin kula da barace-barace akan hanyoyi.
Hajiya Hassana Jummai mace ce mai sha’awar lambu, ziyara da taimakon jama’a. Bayan nan tana da sha’awar ziyarce-ziyarce inda ya kaita ga ziyarar kasar Amurka, Dubai, Belgium, da kasar Ghana, Afrika ta kudu da kasar Saudiya.
Mama kamar yadda al’ummar Bargawa ke kiranta mace ce mai kwazo da son taimakon jama’a, nasabarta da sarautar Bargu ya kai ta da samun sarautar YUN WURE kamar dai ka ce Sarauniyar Matan Bargu, tana da aure da ‘yaya har da jikoki.
Ta halarci tarukan karawa juna sani da dama a fage daban-daban. YUN WURE uwa ce da a ko yaushe tana bukatar kasancewa tare da yara dan kulawa da tarbiya da raino.
Har yau jiki bai gaji ba, domin kusan a kowani lokaci tana tsaye ne, ganin hakan ya sa ta ke muradin zama da jama’a don sanin halin da su ke ciki da irin gudunmawar da ya kamata ta bayar.

Exit mobile version