Hatsabibi: Yadda Aka Yi Musayar Maitangaran Da Matan Dapchi

Daga  Umar A. Hunkuyi

Bayanai sun bayyana kan yadda Jami’an tsaro na SSS, suka yi musayar fursuna da bangaren Boko Haram, na al-Barnawi, bisa sharadin a sakan masu wani babban kwamanda na su, Hussaini Maitangaran, su kuma su saki yara mata, ‘yan makarantar Dapchi.

LEADERSHIP A Yau, ta kawo rahoton kama Maitangaran din da Jami’an tsaron na SSS, suka shelanta a cikin wani bayani da suka fitar ranar 9 ga watan Satumba 2017, wanda aka ce shi ya kitsa harin bamabaman da aka kai a Kano.

A wata makala da Ann Mcgregor, wata kwararra a fannin sha’anin tsaro na duniya ta fitar, a shafin ta na yanar gizo mai suna, News Plus Biews, ta yi karin haske kan yadda wasu ‘yan Nijeriya da abokanan huldan su na waje, suke cin kazamar riba kan kudaden musayar da suke shiryawa ana yi da ‘yan ta’addan.

“Tun a shekarar 2009 ne gwamnatin ta Swiss ta mayar da kan ta wata ‘yar baruwanmu ta musamman, wacce take shiga tsakani a rigingimu da yawa da ake yi a kasashen Afrika. “Wanda kuma ake biyan ta kudi kan hakan, amma wanda ya fi janyo hankali da tayar wa da gwamnatocin kasashen Turai da Amurka hankali, shi ne wanda wai aka ce, ta shiga Tsakani domin tsagaita wuta da kuma sakin yara mata ‘yan makarantar Dapchi.”

“Inda saka da warwaran take shi ne, hanyar da aka bi wajen sace ‘yan matan, da kuma hanyar da aka bi wajen sakin su. ‘Yan ta’addan na Boko Haram, suna rike da daliba guda, Leah Sharibu, daga cikin ‘yan mata 110 da suka sace, domin ta ki fita daga addininta na Kirista.

“Sai dai kuma, wata majiya ta Jami’an sirri, sun tabbatar da cewa, ‘yan ta’addan na Boko Haram, da masu shiga tsakanin na Swiss da kuma abokanan burmin na su ‘yan Nijeriya, har yanzun suna neman gwamnatin ta Nijeriya da ta kara biyan su wasu kudade domin su biya fansa, ta kuma saki wasu manyan Kwamandojin sashen na al-Barnawi, su shida da ke tsare a hannun Jami’an tsaro na DSS. Wanda hakan ke kara tayar da hankali.

“Damuwar ita ce, ta zargin hadin baki da kuma cuwa-cuwa, a tsakankanin ‘yan Nijeriyan da ke shiga tsakani, da suka hada da, Babban Daraktan hukumar ta DSS, Mista Lawal Daura, da Ministan harkokin cikin gida, Janar Abdurrahman Dambazau, Ambassada Babagana Kingibe, da kuma mai shirya alakar da kasashen wajen, kuma Shugaban Ma’aikata a Fadar ta Shugaban Kasa, Abba Kyari. A bangare guda kuma, Ofishin Jami’an Ofishin Jakadancin Kasar ta Swiss da ke Nijeriya, da Jami’an tsaro na sashin Ma’aikatar harkokin waje na kasar ta Swiss.

“Wani Jami’in tsaro na farin kaya na Swiss din, Pascal Holliger, tare da mutanan cikin kasar nan, Mustapha Zannah, wanda Lauya ne, yana kuma da wata makaranta a Maiduguri, inda yake bayar da karatu kyauta ga marayun mutanan da rikicin na Boko Haram ya daidaita, wacce kuma wata kungiyar bayar da tallafi ce ta kasar Saudiyya ta kafa take kuma daukan nauyin ta, tana kuma cikin jerin cibiyoyin da kasar Amurka ke baiwa tallafi, da kuma Aisha Wakil, su ne suka shirya yanda aka yi musayar, bayan an biya ‘yan ta’addan Yuro milyan 5, gami da wasu manyan kwamandojin su da ke tsare a hannun Lawal Daura,din.

“Kawo yanzun, babban ladar da aka baiwa ‘yan ta’addan na Boko Haram, shi ne ta Hussaini Maitangaran, wanda shi ne ya kitsa tare da jagorantar hare-hare da kashe-kashe da dama a Kano, da suka hada da, harin da aka kai a babban Masallacin Juma’a na tsakiyar birnin na Kano, inda aka kashe sama da mutane dubu guda. A ranar 31 ga watan Agusta 2017 ne, Jami’an tsaron na DSS suka kama shi. A matsayin wani bangare na musayar da ‘yan matan na Dapchi,” duk kamar yadda Ann din ta zayyana cikin makalar na ta ta ranar 28 ga watan Maris.

A cewar Jami’an tsaron na SSS, cikin bayanin da suka fitar a watan Satumba 2017, Maitangaran, sanannen babban Kwamanda ne a cikin kungiyar ‘yan ta’adda ta, ‘Islamic State of West Africa,’ ISWA, “Yana cikin jerin wadanda Sojojin Nijeriya ke nema ruwa a Jallo, tun 2012, lokacin da ya jagoranci kai hari Ofishin Mataimakin Shugaban ‘Yan Sandan Nijeriya, AIG, da ke Zone 1, ranar 20 ga watan Janairu 2012, da kuma hare-hare a wasu sassa na garin Kano. Maitangaran din ne kuma ya jagoranci harin da aka kai ranar Juma’a kan masallata a Babban Masallacin Juma’a na garin Kano, da kuma hare-haren da aka kai a wasu cibiyoyin Sojoji a Jihar Yobe a 2015, inda aka kashe Daruruwan mutane.”

Jami’an hukumar na SSS, a shekarar da ta gabata ce suka ce, Maitangaran din kwararre ne wajen iya hada bamabamai, wanda kuma ya kware wajen iya zugawa da kuma shirya wasu su kai harin kunar bakin wake da jefa bamabamai a yankin na Arewa maso gabas.

Exit mobile version