Babban Manajan Hukumar kula da Tashoshin Jiragen Ruwa a Legas LASWA Mista Oluwadamilola Emmanuel, ya sanar da cewa, an gano gawarwakin Fasinjoji 15 da suka bace bayan da jirgin ruwa da ke dauke da fasinjojin 16 ya kife a yankin Ojo da ke a ranar 8 ga watan Yuli 2022.
Mista Emmanuel a jiya Lahadi ya kuma tabbatar da cewa, an gano gawarwakin fasinjoji 11 kari da wasu gawarwaki 4 na fasinjojin.
- Zabar Mataimaki: Tinubu Ya Watsa Wa Gwamnonin Arewa Maso Yamma Kasa A Ido
- Zabin Shettima A Matsayin Mataimakin Tinubu Mataki Ne Mafi Cancanta- In ji Zulum
A cewar Mista Emmanuel, masu ceto daga hukumarsa ta LASWA da wasu masu ceto daga hukumar kula da rafukan ta kasa da kuma daga hukumar bayar da agajin gaggawa na ci gaba da neman sauran gawarwakin fasinjojin da iftila’in na harin jirgin ya rutsa da su
Mista Emmanuel, ya sanar da cewa hatsarin ya auku ne a yayin da jirgin ke kan hanyar sa ta zuwa Ibeshe da ke a yankin bayan kadawar igiyar ruwa da ta janyo jirgin ya jefar da fasinjojin da ke cikinsa.