A ƙalla mutane 20 ne suka rasa rayukansu bayan jirgin ruwan katako ya kife yayin da yake ɗauke da fasinjoji daga ƙaramar hukumar Agatu a Jihar Benue zuwa Jihar Nasarawa.
Mafi yawancin waɗanda suka rasa rayukansu ‘yan kasuwa ne, yayin da suke dawowa daga Kasuwar Ocholonya a Agatu. Shaidu sun bayyana cewa jirgin ruwan ya kasance cike da kaya da fasinjoji, waɗanda suka kasance ‘yan kasuwa daga Nasarawa.
- Kotu Ta Sake Dakatar Da Sarki Ado Daga Gyara Fadar Nassarawa
- EFCC Ta Tsare Tsohon Gwamnan Kogi, Yahaya Bello
Wani shaida ya ce jirgin ya bugi wani itace ne a cikin Kogin Benue, inda nan take ya fashe, hakan ya haifar da mutuwar fiye da 20, ciki har da mata da yara.
Masu ceto daga yankin sun gudanar da aiki, inda aka samo gawarwaki fiye da 20. Shugaban ƙaramar hukumar Agatu, Melvin Ejeh, ya tabbatar da lamarin, yana cewa an samu gawarwaki fiye da 20, kuma ana ci gaba da aikin ceto.