Daga Bello Hamza
An tabbatar da mutuwar mutum 19 a wani mummunan hartsarin mota da ya auku a kan hanyar Sakkwato zuwa Gusau ranar Alhamis.
Hatsarin ya uku ne tsakanin mota kirar ‘Bolkswagen Golf’ mai rajista da karamar hukumar Sokoto-North da kuma mota Bas kira ‘Toyota Hiace’ mai rajista da karamar hukumar Bodinga.
Kamar dai yadda jami’in watsa labarai na rundunar ‘yan sanda jihar Sakwatto, DSP Muhammad Sadik, ya bayyana, ya kuma ce, hatsarin ya auku ne a kauyen da ake kira Bimasa a karamar hukumar Tureta da misalin karfe 4:30 na yamma ranar Alhamis.
Ya kara da cewa, an zarce da wadanda suka mutu da kuma wadanda suka ji ciwon zuwa asibitin koyarwa na Jami’ar Usmanu Danfodiyo.