Rundunar ‘yansandan jihar Kano, ta kama wasu ‘yan daba 54 da ake zargi da yunkurin kawo cikas ga Hauwan Daushe a yayin bukukuwan sallah a jihar.
Kwamishinan ‘yansandan jihar, Usaini Gumel ne, ya bayyana haka a wata hira da kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) a ranar Alhamis.
- Dalilan Da Ya Sa Ba Ma Daukar Alkalan Wasan Nijeriya – FIFA
- Yadda Jami’in Tsaro Ya Bindige Wani Mutum Ana Tsaka Da Sallar Idi A Zamfara
“Mun kama mutane 54 dauke da muggan makamai da ke shirin kawo cikas ga bukukuwan sallah da ke gudana a sassan jihar.
“An kwato abubuwa da suka hada da wiwi, babura da wasu muggan makamai da sauransu daga hannunsu.
“Muna da bayanan sirri da ke nuna cewa wasu matasa suna taruwa da nufin kai hari a karkashin jagorancin ‘yan siyasa a jihar.
“Sun shirya kai farmaki yayin Hawan Daushe da wasu bukukuwa a jihar.
“Muna shawartar ‘yan siyasa da su gargadi magoya bayansu kan shirin kai kowane irin farmaki,” in ji shi.
Kwamishinan ya ce, hadin gwiwar hukumomin tsaro sun dauki matakan tsaro da suka dace domin tunkarar duk wani da ke shirin kawo tsaiko a lokacin Hawan Daushe da bayansa a jihar.