• English
  • Business News
Sunday, October 19, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Hawayen Munafurci

by CGTN Hausa
2 years ago
Hawayen munafurci

Yanzu haka musulmi a sassan duniya na cikin watan Ramadan mai tsarki. A daidai wannan lokaci, sakataren harkokin wajen kasar Amurka Antony Blinken ya fitar da sanarwa a kwanan baya, inda ya yi wa al’ummar musulmi gaisuwar watan Ramadan, tare da bayyana cewa, “musulmai ‘yan kabilar Uygur a jihar Xinjiang ta kasar Sin, da ‘yan kabilar Rohingya na kasashen Myanmar da Bangladesh, da Palesdinawa na zirin Gaza, suna fama da rikice-rikice da wahala.”

Ba wani abu da ya fi “hawayen munafurci” dacewa da siffanta wannan sanarwar da Mr.Blinken ya bayar, sabo da tun bayan barkewar rikici a tsakanin Palasdinu da Isra’ila a wannan karo, duk da tsanantar yanayin jin kai a zirin Gaza, Amurka ta yi ta rura wutar rikicin, a sa’i da kuma take “kuka”.

  • Xi Ya Jajantawa Takwaransa Na Rasha Game Da Harin Ta’addanci Da Ya Auku A Moscow Oblast
  • Ba Za Mu Lamunci Amfani Da Yunwa A Matsayin Makamin Yaki A Gaza Ba – Tarayyar Turai

Kasancewarta babbar kawar Isra’ila da ma kasar da ta fi samar mata makamai, tun bayan barkewar rikicin, Amurka ta yi ta kara samar da gudummawar soja ga Isra’ila. Bisa rahoton da kafofin yada labarai na kasar ta Amurka suka bayar, an ce, ya zuwa yanzu, gwamnatin Biden ta sayar da makaman soja fiye da sau 100 a asirce ga Isra’ila, ciki har da makamai sama da dubu 10, matakin da ya sa masana’antun samar da makamai da ma masu ruwa da tsaki na kasar suka ci kazamar riba. Duk da mummunan yanayin jin kai da ake ciki a Gaza, sau hudu Amurka ta na jefa kuri’ar nuna rashin amincewa da kudurin da aka gabatar ga kwamitin sulhu na MDD dangane da tsagaita bude wuta a zirin Gaza. Sai kuma a kwanakin baya, ita Amurka din ta gabatar da wani daftarin kuduri ga kwamitin sulhu dangane da batun tsagaita bude wuta a zirin Gaza, amma a maimakon ta ce a tsagaita bude wuta nan da nan, sai ta gindaya sharuda ga tsagaita bude wuta, wanda ya saba wa daidaiton da akasarin mambobin kwamitin sulhun suka cimma, don haka, ba a kai ga zartas da shi ba.

Amma ga shi yanzu, Mr.Blinken ya fara damuwa da yanayin da Palasdinawa a zirin Gaza ke ciki, shin da gaske ne ya damu? Ba shakka ba haka ba ne, sabo da a kafin ya ambaci Pasdinawa, Mr.Blinken ya fara ne da ambaton “musulmai ‘yan kabilar Uygur a jihar Xinjiang ta kasar Sin”, lallai ainihin burinsa ke nan ya fake da sunan kulawa da yanayin da Palasdinawa a zirin Gaza ke ciki da ma hakkin musulmi don dakile kasar Sin ta hanyar amfani da wai yanayin da ‘yan kabilar Uygur ke ciki a jihar Xinjiang.

Amma karya fure take ba ta ‘ya’ya, duk wadanda suka taba zuwa jihar Xinjiang, ciki har da masana na kasashen yamma da ‘yan jarida da jakadu na kasashen musulmi dake kasar Sin, sun gano cewa, ana samun zaman lafiya da bunkasuwar tattalin arziki da zaman jituwa a tsakanin mabiya addinai daban daban a yankin Xinjiang na kasar Sin, kuma ana tabbatar da hakkin dan Adam na daukacin jama’a, ciki har da ‘yan kabilar Uygur. A hakika, babu rikici a yankin Xinjiang na kasar Sin, zirin Gaza ne ke fuskantar rikice-rikice. Haka kuma musulmai na yankin Xinjiang ba sa fama da yunwa ko kisa, amma miliyoyin musulmai na zirin Gaza suna fama da wadannan matsaloli.

LABARAI MASU NASABA

Labarin Xinjiang A Zane: Aikin Yawon Shakatawa Na Kara Samar Da Arziki Ga Al’ummar Xinjiang

Rashin Amincewa Da Kasashen Yamma Yana Haifar Da Sabon Tunani Kan Huldar Kasa Da Kasa

Sama da kwanaki 160 ke nan tun bayan barkewar rikici a tsakanin Palasdinu da Isra’ila, wanda ya sa fararen hula sama da dubu 32 suka rasa rayukansu, baya ga miliyoyin dake fama da yunwa. Kamata ya yi Amurka ta daina wasan siyasa da yanayin jin kai na zirin Gaza. Abin da ya kamata ta yi shi ne ta dauki hakikanan matakai na ceton rayukan musulmai a Gaza, a maimakon ta fitar da sanarwa maras ma’ana.

 

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Labarin Xinjiang A Zane: Aikin Yawon Shakatawa Na Kara Samar Da Arziki Ga Al’ummar Xinjiang
Ra'ayi Riga

Labarin Xinjiang A Zane: Aikin Yawon Shakatawa Na Kara Samar Da Arziki Ga Al’ummar Xinjiang

October 13, 2025
Rashin Amincewa Da Kasashen Yamma Yana Haifar Da Sabon Tunani Kan Huldar Kasa Da Kasa
Ra'ayi Riga

Rashin Amincewa Da Kasashen Yamma Yana Haifar Da Sabon Tunani Kan Huldar Kasa Da Kasa

October 12, 2025
Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka
Ra'ayi Riga

Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka

October 7, 2025
Next Post
NDLEA Ta Kwace Maganin Cutar Hauka Mai Nauyin Kilo 150 A Gombe

Hukumar NDLEA Ta Tarwatsa Wasu Kungiyoyin Ta'ammuli Da Hodar Iblis A Abuja Da Kano

LABARAI MASU NASABA

gombe

Ɗaliban Jihar Gombe Sun Samu Ƙarin Kashi 100 Na Kuɗin Tallafin Karatu

October 18, 2025
Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma

Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma

October 18, 2025
An Bude Taron Sanin Makamar Aiki Na Cika Shekaru 80 Da Kafuwar MDD A Wuhan Na Kasar Sin

An Bude Taron Sanin Makamar Aiki Na Cika Shekaru 80 Da Kafuwar MDD A Wuhan Na Kasar Sin

October 18, 2025
Tsadar Rayuwa Da Karuwar Ta’addanci Na Ci Gaba Da Tagayyara ‘Yan Nijeriya

DHQ Ta Ƙaryata Rahoton Yunƙurin Yi Wa Tinubu Juyin Mulki

October 18, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: ‘Yansanda Sun Tarwatsa Masu Zanga-zangar Adawa Da Dokar Ta-ɓaci A Ribas

‘Yansanda Sun Kai Samame Maboyar ‘Yan Ta’adda, Sun Kwato Miyagun Kwayoyi A Gombe

October 18, 2025
Kamfanin Gine-Gine Na CCECC Ya Fara Gina Wani Titin Mota Da Zai Rage Cunkoso A Birnin Abuja Na Tarayyar Najeriya

Kamfanin Gine-Gine Na CCECC Ya Fara Gina Wani Titin Mota Da Zai Rage Cunkoso A Birnin Abuja Na Tarayyar Najeriya

October 18, 2025
ASUU

Cikin Wata 9 Farfesoshi 309 Sun Bar Aiki A Jami’o’in Gwamnati, In Ji ASUU

October 18, 2025
Masanin Ilimin Physics Chen Ning Yang Ya Rasu Yana Da Shekaru 103

Masanin Ilimin Physics Chen Ning Yang Ya Rasu Yana Da Shekaru 103

October 18, 2025
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

October 18, 2025
Kasar Sin Ta Gargadi Amurka Game Da Yunkurin Samarwa Yankin Taiwan Makamai

Kasar Sin Ta Gargadi Amurka Game Da Yunkurin Samarwa Yankin Taiwan Makamai

October 18, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.