ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, June 4, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Hayaniya ‘Yar Facebook!

by Sulaiman Bala Idris
1 week ago
Facebook

Idan ba ka da wadata irin ta haƙuri, ka rufa wa kanka asiri wurin taƙaita irin nau’in mutanen da za ka yi mu’amala da su a sahar sada zumunta ta ‘Facebook’. 

Zai yiwu, duk da ba ni da tabbaci. Daga cikin dalilan da suka sa hukumar gudanarwar Facebook ta ke ta kokaren lalubo hanyoyin samar da ƴanci ga masu mu’amala da kafar, shi ne don a baka ikon yin tankaɗe da rairaya daidai da ɗanɗanonka da son ranka. 

A fannin ilimin kimiyyar zamantakewa da sanin halayyar ɗan adam, mun tafi kan cewa, an halicci mutane da bambancin gaske a tsakaninsu, wani dogo ne baƙi; wani kuma gajere ne fari. Wani na da daƙwalen idanu, da manyan kunnuwa. Wani sai ka ga an yi shi da idanu ƴan mitsi-mitsi kamar ɗan Chana. Wannan iko ne na Allah mai halitta. Saboda ba ka da zaɓin yadda ka ke so a halitto ka. 

ADVERTISEMENT

Bayan an yi maka zubi ta mutum, ba ya yiwuwa ka cika kuma ka amsa sunan mutum har sai ka gina ‘ƊABI’A’. Ita ɗabi’a (duk da akwai taƙaddama mai ƙarfi kanta) kaso mafi tsoka daga gareta koyonsu ake yi. Ɗabi’a ita ce ke samar da mutum. Ita ke tasirantuwa a zuciyarsa, ta tasirantu a ganinsa, ta tasorantu a jinsa, sannan ta tasirantu a tunaninsa da fahimtarsa.

Idan kana so, da zaran ka haɗu da mutum za ka iya karantar wanne iri ne shi, wannan kuwa ta hanyar nazarin ɗabi’arsa. Saboda ita ke juya komi na rayuwarmu. Idan mutum dolo ne, kana ganinsa za ka fahimci cewa ya tasirantu da rayuwa cikin dolaye. Idan maƙetaci ne, ya koyi ƙeta daga gida, ko wurin abokai, ko a makaranta, ko a unguwa. Idan ka ga mai natsuwa da kamun kai – ya koya ne walau a gida, ko a makaranta, ko wurin abokai.

LABARAI MASU NASABA

No Content Available

Mutane da yawa za su so su kasance cikin jerin masu natsuwa da kamun kai. Ba nan gizo ke saƙar ba. Iya kiyayewa da kare kamun kai ne abu mai wahala. Abu kaɗan na iya tunzura ka ka rushe kamun kan da ake kallonka da shi. Duk natsuwarka, kana iya aikata abu guda ko ka furta wata kalma da za ta sauke ka daga wannan matsayin a idon jama’a.

Akwai irin waɗannan misalai masu tarin yawa, waɗanda ke nuni da yadda za ka ga mutum mai natsuwa da kamun kai, amma ya gaza kiyaye kuɓecewarsu daga gare shi. 

A hayaniya ƴar facebook, za ka taras da mutane mabambanta, kowa da irin ɗabi’arsa. Wani ƙwararre ne a harkar gardama, ga naci da kafiriɗin sai an san da zamansa. A komi yana da ra’ayi, sannan duk wanda ya bambanta da shi a mahanga, an yi ta jinsu kenan.

Babbar matsalar hayaniya ƴar Facebook shi ne mutane sun ɗauka cewa, gardama da soke-soke suna iya sauya tunani, mahanga, ko fikirar da suka cakuɗu da ɗabi’a wurin ginuwa. Shi ya sa a farkon rubutun nan na ɗan yi sharar fage dangane da ɗabi’a. Domin a ƙa’ida ta hankali shi ne, kafin ka hukunta mutum, yana da kyau ka san ɗan wani abu dangane da ɗabi’arsa. Idan mutum ya ce, ga matsayarsa ko fahimtarsa, kai kuma kana da wata matsayar ta daban. Mene ne abin zagi, da hauragiya? Ai kamar yadda hancinku da zubin kunnuwanku ba iri guda ba ne, haka ɗabi’arku. 

A irin hayaniya ta Facebook ne za ka ga tsagera mai tulin ilimi, shi burinsa kawai manya su karkace ya ɗare kan wuyansu ya yi ta tsalle yana ɗiban albarka. Tarin karatu ba shi ke nufin kana da lasisin saitawa ko gina ɗabi’ar wanda kuka saɓa da shi. 

A hayaniyar Facebook ne za ka ga mutum da tarin shekaru, sai ya riƙa fakewa da girma yana sa kansa a gurbin hedimastan kula da abin da wasu (musamman waɗanda ya sani) suke aikatawa. Ya yi ta katsalandan, har ta kai an fara keta rigar shekarunsa.

Yana da kyau mu fahimci cewa, ‘DON SHIRU A KE TSORON GAWA’, a wasu lokutan mafi alheri garemu da mutuncinmu shi ne yin shiru. Idan a komi sai mun yi tsokaci ko mun saki baki, za  mu riƙa haifarwa da kanmu kafofin da za a keta mu. Abu mafi sauƙi a hayaniyar Facebook shi ne ka yi magana kan wani lamari da ke faruwa, sai wani ya yi kwament  da ‘Ƙarya ne’. shi kuwa duk wanda aka cewa maƙaryaci, za a iya watso mishi kowacce irin baƙa.

Idan kana facebook, ka buɗe zuciyarka, ka kuma faɗaɗa hangenka. Domin wuri ne da ke cike da hayaniya da rashin hankali, Facebook kafa ce da ke ɗauke da masu tarin karatu amma ba natsuwa. Ga tulin Masanan da basu da saiti. Tsaf! Za a kifar da kai ta baibai. Idan kai mai yawan fushi ne, shi kenan an gamu! Don kullum ka yi ta kumbure-kumbure kenan, domin hayaniya ƴar Facebook ba ta ƙarewa. Kullum akwai maudu’i. 

Mu haɗu mako mai zuwa!

Facebook
Sulaiman Bala Idris
+ postsBio
  • Sulaiman Bala Idris
    https://hausa.leadership.ng/author/sulaiman-bala-idris/
    Mummunan Zato
  • Sulaiman Bala Idris
    https://hausa.leadership.ng/author/sulaiman-bala-idris/
    Me Ake Nufi Da Ado? 
  • Sulaiman Bala Idris
    https://hausa.leadership.ng/author/sulaiman-bala-idris/
    Gwamna Dauda Lawal A Shekara 60: Inda Akwai Fata, Akwai Mafita
  • Sulaiman Bala Idris
    https://hausa.leadership.ng/author/sulaiman-bala-idris/
    Yawaitar Al’umma: Martanin Karl Marx Ga Rabaran Malthus

MASU ALAKA

No Content Available
Next Post
Taron Ministocin Cinikayya Na APEC Ya Yi Kira Da A Samar Da Matsaya Daya Ta Hadin Gwiwar Tattalin Arziki Da Cinikayya

Taron Ministocin Cinikayya Na APEC Ya Yi Kira Da A Samar Da Matsaya Daya Ta Hadin Gwiwar Tattalin Arziki Da Cinikayya

Discussion about this post

LABARAI MASU NASABA

Tawagar Masanan Dakile Yaduwar Cututtuka Ta Sin Ta Isa DR Congo

Tawagar Masanan Dakile Yaduwar Cututtuka Ta Sin Ta Isa DR Congo

June 3, 2026
Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli

Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli

June 3, 2026
Han Zheng Zai Halarci Taron SPIEF Karo Na 29 A Rasha Tare Da Gudanar Da Ziyarar Aiki A Belarus

Han Zheng Zai Halarci Taron SPIEF Karo Na 29 A Rasha Tare Da Gudanar Da Ziyarar Aiki A Belarus

June 3, 2026
Majalisa Ta Nemi Tinubu Ya Canza Dabarun Yaƙi Da Ta’addanci Don Kawo Ƙarshen Kashe-kashe

’Yan Majalisar Tarayya 3 Sun Fice Daga APC Zuwa ADC da PRP

June 3, 2026
An Fara Watsa Shirye-Shirye Masu Taken “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” Da Sauran Fina-Finan Bayyana Labaran Sin A Kasar Laos

An Fara Watsa Shirye-Shirye Masu Taken “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” Da Sauran Fina-Finan Bayyana Labaran Sin A Kasar Laos

June 3, 2026
Tambuwal Ya Jajanta Wa Waɗanda Harin ’Yan Bindiga Ya Shafa A Sokoto, Ya Nemi A Ƙara Tsaro

Tambuwal Ya Jajanta Wa Waɗanda Harin ’Yan Bindiga Ya Shafa A Sokoto, Ya Nemi A Ƙara Tsaro

June 3, 2026
Gwamnatin Beijing Ta Amince Da Kafa Cibiyar Kirkire-Kirkiren Fasahar Lissafi Mai Nasaba Da Sararin Samaniya

Gwamnatin Beijing Ta Amince Da Kafa Cibiyar Kirkire-Kirkiren Fasahar Lissafi Mai Nasaba Da Sararin Samaniya

June 3, 2026
Za A Fara Buga Gasar Kofin Sarkin Gombe Bayan Masu Ruwa Da Tsaki Sun Cimma Matsaya

Za A Fara Buga Gasar Kofin Sarkin Gombe Bayan Masu Ruwa Da Tsaki Sun Cimma Matsaya

June 3, 2026
Hada Kai Da ’Yan Awaren Yankin Taiwan Ba Zai Haifar Da Ɗa Mai Ido Ba

Hada Kai Da ’Yan Awaren Yankin Taiwan Ba Zai Haifar Da Ɗa Mai Ido Ba

June 3, 2026
An Gudanar Da Taron Kasa Da Kasa Na Magadan Gari Na 2026 A Beijing

An Gudanar Da Taron Kasa Da Kasa Na Magadan Gari Na 2026 A Beijing

June 3, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.