ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamna Dauda Lawal A Shekara 61:Shugaban Da Ke Gudanar Da Mulki Bisa Kyakkyawar Manufa

by Sulaiman Bala Idris
5 days ago
Dauda

Da a ce an tambaye ni, shin Dauda Lawal din da na sani shekaru biyar da suka gabata shi ne wannan Dauda Lawal na yau? Babu shakka, da babban harafi zan ce: A’A.

Lokacin da Dauda Lawal ya cika shekaru 55 a shekarar 2020, na rubuta wata kasidar yabo mai taken “The Dauda Lawal I Know” — wato “Dauda Lawal Din Da Na Sani.” A wancan lokacin, na bayyana shi a matsayin mutum mai zurfin fahimtar yadda huldar mutane ke tsara rayuwar al’umma; tsohon ma’aikacin banki ne da ya kai kololuwar sana’arsa, ya yi ritaya yana neman rayuwa mai natsuwa da sirri, kamar yadda Hausawa kan ce, “ba hayaniya.”

Amma kaddara ta kawo wani sabon babi.

ADVERTISEMENT

A shekarar 2021, duk da irin yakin neman bata masa suna da aka yi, Dauda Lawal ya amsa kiran al’ummar Zamfara da ke cikin mawuyacin hali. Kukan nasu shi ne: “Dauda, ka taimake mu.”

A lokacin da nake kallon Dauda Lawal na shekarun 2018 zuwa 2023, na san shi ne mutum mai kallon al’amuran al’umma daga matakin daidaikun mutane; yana fahimtar yadda huldar yau da kullum tsakanin mutane ke haifar da abin da al’umma take dauka a matsayin gaskiya. Wannan fahimta ba abin mamaki ba ce idan aka yi la’akari da doguwar gogewarsa a harkar banki, inda ya kai matsayin da ya yi fice a sana’arsa.

LABARAI MASU NASABA

Karuwar Farin Jinin Gwamna Umaru Bago A Siyasar Jihar Neja

Kyakkyawan Tsarin Laken Asiri Zai Dakile Shirin Magudin Zabe A Nijeriya —Mohammed

Amma tun daga ranar 29 ga Mayun 2023, na fara ganin wani sabon Dauda Lawal gaba daya.

Da ba don ilimin da ya samu a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ba, da zan yi zaton cewa ya yi karatun ilimin zamantakewa kai tsaye ne wajen manyan malaman fannin, kamar Auguste Comte, Herbert Spencer da Emile Durkheim, har ma da malaman zamani da suka zurfafa nazarin yadda tsarin al’umma ke aiki.

A cikin shekaru ukun da muka yi a gwamnati, yayin da Dauda Lawal ke jagorantar Jihar Zamfara, na ga yadda yake tafiyar da mulki ba tare da gaggawa ko hayaniya ba, sai dai cikin tsari, natsuwa da mayar da hankali kan sakamakon da ake son cimmawa.

A gare ni, wannan shi ne Functionalism — wata muhimmiyar ka’ida a ilimin zamantakewa — tana bayyana kanta a aikace.

Na ga gwamna wanda ya fahimci tunanin Auguste Comte cewa al’umma ba tarin mutane ne kawai ba, face wata halitta ce mai hadin gwiwar sassa daban-daban. Tsaro, ilimi, lafiya, tattalin arziki da sauran cibiyoyi duk suna da alaka da juna; kowanne yana da rawar da yake takawa wajen tabbatar da tsarin al’umma ya ci gaba da tafiya yadda ya kamata, kamar yadda gabobin jiki ke aiki tare domin rayuwa ta dore.

Mutum na iya yin jayayya da ni, amma abin da na gani shi ne gwamna da ya fahimci abin da Comte ya kira “Positibe Philosophy” — wato dogaro da hujjoji, bayanan zahiri da lura da abubuwan da ke faruwa wajen fahimtar matsalolin al’umma da kuma nemo hanyoyin magance su, maimakon dogaro da zato ko hasashe kawai.

Kuma Dauda ya yi amfani da wannan fahimta wajen gudanar da jihar.

Misali mafi bayyana shi ne yadda Kudaden Shigar Cikin Gida (IGR) na Zamfara suka tashi daga kusan Naira miliyan 90 a wata zuwa sama da Naira biliyan biyar a wata.

Wata rana, dole ne na je dakin karatun Gwamna Dauda na binciki littattafansa domin sanin cewa: shin yana da littafin Emile Durkheim mai suna Rules of Sociological Method da kuma Sociological Theory na George Ritzer ne?

Na shafe shekaru ina nazarin ra’ayoyin Talcott Parsons, kuma idan na kalli salon jagorancin Dauda, ina ganin yadda ka’idar Structural Functionalism ta bayyana a aikace, musamman abin da Parsons ya kira AGIL Scheme.

A fahimtar Parsons, domin al’umma ta ci gaba da wanzuwa, dole ne tsarin mulkinta da cibiyoyinta su iya yin abubuwa hudu: daidaita kansu da yanayin da suke ciki, cimma manufofin da aka sanya, tabbatar da hadin kai, da kuma kare tare da sabunta muhimman dabi’u da ka’idojin da al’umma ta ginu a kansu.

Dauda Lawal ya nuna wadannan abubuwa a salon da yake tafiyar da Zamfara.

Na farko, daidaitawa da yanayi.

A wajen Dauda, wannan ya fara ne da fahimtar cewa Zamfara na bukatar taimakon masu bayar da tallafin ci gaba na kasashen waje, musamman saboda an daina amincewa da jihar a baya sakamakon matsalolin rashin gaskiya da bayyana yadda ake tafiyar da harkokin gwamnati.

Daga cikin wadanda aka sake jawo hankalinsu akwai Bankin Duniya. Dauda ya tuntube su, ya samar da yanayin da zai sa su sake yarda da jihar, kuma aka dawo da wasu ayyukan ci gaba tare da tallafa musu.

Na biyu, cimma manufofi.

Ga Dauda, shugabanci ba wai zama a ofis da jiran abubuwa su faru ba ne. Yana nufin sanin abin da gwamnati take son cimmawa tun daga farko, sannan a tsara yadda ma’aikatu da hukumomi za su hada kai wajen cimma wadannan manufofi.

Na uku, hadin kai.

Gwamnati ba za ta iya yin aiki yadda ya kamata ba idan kowanne sashe yana tafiya da kansa. Saboda haka, Dauda yana kokarin tabbatar da cewa ma’aikatu da hukumomi suna aiki tare, ana warware sabani, kuma ana tafiyar da gwamnati a matsayin tsari guda.

Na hudu, kare muhimman manufofi da dabi’u.

A nan ne na fi ganin fahimtar Dauda game da abin da Parsons ya kira Latency. Gwamnatinsa ta ginu ne a kan manufar ceto Zamfara da sake gina ta. Saboda haka, ba wai ana gudanar da ayyukan gwamnati ne kawai ba; ana kuma kokarin tabbatar da cewa wannan manufa ta ci gaba da zama tushen duk abin da gwamnati take yi.

Ina fatan zan iya rubuta abubuwa da yawa fiye da haka. Amma, in Allah Ya yarda, a shekaru masu zuwa, duk ranar 2 ga Satumba, zan sake komawa kan wasu abubuwan da ban samu damar bayyana su a baya ba, domin girmama mutumin da a yau ba na kallonsa a matsayin shugaba ko mai gida kawai ba, ina kallonsa a matsayin uba.

Barka da cika shekaru 61 da haihuwa, Gwamna Dauda Lawal.

Jagorancinka ya sauya alkiblar Jihar Zamfara, ya kuma taimaka wajen sauya mummunan labarin da aka dade ana yadawa game da jihar.

Dauda
Sulaiman Bala Idris
+ postsBio
  • Sulaiman Bala Idris
    https://hausa.leadership.ng/author/sulaiman-bala-idris/
    ‘Symbolic Interactionism’:Sabuwar Makaranta A Kimiyyar Zamantakewa
  • Sulaiman Bala Idris
    https://hausa.leadership.ng/author/sulaiman-bala-idris/
    Hayaniya ‘Yar Facebook!
  • Sulaiman Bala Idris
    https://hausa.leadership.ng/author/sulaiman-bala-idris/
    Mummunan Zato
  • Sulaiman Bala Idris
    https://hausa.leadership.ng/author/sulaiman-bala-idris/
    Me Ake Nufi Da Ado? 

MASU ALAKA

Gwamnatin Neja Ta Bayar Da Umarnin Kawo Karshen Matsalar Tsaro
Rahotonni

Karuwar Farin Jinin Gwamna Umaru Bago A Siyasar Jihar Neja

September 5, 2026
Kyakkyawan Tsarin Laken Asiri Zai Dakile Shirin Magudin Zabe A Nijeriya —Mohammed
Rahotonni

Kyakkyawan Tsarin Laken Asiri Zai Dakile Shirin Magudin Zabe A Nijeriya —Mohammed

September 5, 2026
Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
Rahotonni

Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki

September 5, 2026
Next Post
An Bude Baje Kolin Masana’antun Al’adu Da Na Bude Ido Na Kasar Sin Na Shekarar 2026

An Bude Baje Kolin Masana’antun Al’adu Da Na Bude Ido Na Kasar Sin Na Shekarar 2026

LABARAI MASU NASABA

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

September 9, 2026
Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

September 9, 2026
“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

September 9, 2026
’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

September 9, 2026
Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.