ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

‘Symbolic Interactionism’:Sabuwar Makaranta A Kimiyyar Zamantakewa

by Sulaiman Bala Idris
3 months ago

Bayan da Makarantun ‘Functionalism’ da ‘Conflict’ suka gama yayinsu, inda kowannensu ya yi bayanin tsarin zamantakewa daidai da fahimtar makarantarsa, an samu bullar makarantar ‘Symbolic Interaction’ wacce ta zo domin yin bayanin wani muhimmin abu wanda wadancan makarantu biyu suka kawar da kai ga bayaninsa.

Dalton Conley a littafinsa ‘Introduction to thinking like a Sociologist’ ya bayyana cewa, masani Herbert Blumer ne ya sanya wa wannan makaranta suna ‘Symbolic Interactionism’. Domin karin tabbaci, George Ritzer a littafinsa na ‘Encyclopedia of Social Theory’ ba kawai ya tabbatar da batun cewa Blumer ne ya samarwa da makarantar sunan ba, ya fadi shekarar wato 1937, da Blumer din ya kirkiri sunan.

Wannan kuma ba yana nufin sai bayan zuwan Blumer ba ne sannan aka fara yin bayanai masu alaka da ‘Symbolic Interactionism’, tun kafin shi sai da George Herbert Mead ya yi wa wannan makaranta hidima sosai. Rubuce-rubucensa har yanzu suna taka muhimmiyar rawa wurin fahimtar gudummawar makarantar ‘Symbolic Interactionism’ ga rayuwar al’umma, musamman littafinsa na ‘Mind, Self and Society’; littafin da George Ritzer ya yi ikirarin cewa, ya fi kowanne littafi muhimmanci a wannan makaranta.

ADVERTISEMENT

Kafin na shiga bayani, zan so mu fahimci wani abu mai muhimmancin gaske wanda shi ne asasin bambancin da ke tsakanin wadancan makarantu biyu da wannan da za mu yi bayani. ‘Functionalism’ da ‘Conflict’ makarantu ne da suke kallon daukacin al’umma wurin gabatar da bayanansu. Babu ruwansu da dabi’ar mutum a shi daya tilo ko mu’amalarsa tsakaninsa da sauran mutane, suna damuwa ne da abubuwan da ke iko da dabi’u a jam’i da kuma bangarorin al’umma (structures) irinsu bangaren iyali, bangaren ilimi, bangaren soja, bangaren tattalin arziki da sauransu.

Domin cike gibin da wadancan makarantu biyu suka bari ne ya sa aka samar da wannan makaranta ta ‘Symbolic Interactionism’, wacce ta doru bisa fahimta da yin bayani kan mu’amalar da muke gudanarwa ta yau da kullum a tsakaninmu (wato daidaiku) da kuma irin ma’anonin da muke bayarwa ga abubuwan da muke rayuwa da su.

LABARAI MASU NASABA

Buni Ya Nuna Kwarewarsa Ta Diflomasiyya

Shin Tinubu Ya Tabbatar Da Sauke Ribadu Daga Mukaminsa?

A cikin al’umma akwai alamomi da yawa wadanda sune ke saita mu’amalarmu ta yau da kullum. Kuma wadannan alamomin kowannensu yana da yadda ake koyo da fahimtar jingina mishi bayani da muhimmanci. Misali da takalmi, ba kawai don mutum ya fahimci cewa ga wani abu sunanshi takalmi ba shi kenan, a’a dole ne ka fahimci cewa, wani abu ne da mutane ke sanya kafarsu a ciki domin gujewa lalata kafa yayin taka kasa. Don haka mutum idan ya ga takalmi a ganin ido ya san cewa abin sanyawa a kafa ne da ke da muhimmanci a wurinsa.

A wancan misalin na sama, mun fahimci cewa muhimmanta abu a kashin kansa koyo ake yi. Idan ka samu mutanen da babu ruwansu da sanya takalmi don ba su da damuwa ko da kafafunsu za su fashe. Irin wadannan mutanen a wurinsu takalmi ba shi da wata kima ko mutunci.

Babban abin da ya sa mutum ya fi dabba shi ne karfin ikon da yake da shi wurin isar da sako ba tare da ya yi furuci da bakinsa ba. Misali, Kai ne kana tafiya sai ka ga Akuya a gefen titi zaune, ga kuma gawar Zaki a gefe. Ga dukkan alamu Akuyar a firgice take, sai ka nufi wurinta ka tambayeta, shin ke ki ka kashe Zakin nan? Babu amsa.

Toh kwatanta da mutum. Ka zo wucewa sai ka taras da gawa a gefe cikin jini, ga kuma wani mutum a gefe yana kuka kusa da gawar. Ko da ganin mutumin cikin firgici da kaduwa yake. Da ka yi masa magana ba iya amsawa saboda kaduwa. Sai ka tambaye shi, ‘Shin kai ne ka kashe wannan? A nan mun ce mutumin ba ya iya magana saboda firgici. Bambancinsa da dabba shi ne, zai iya bayar da amsa ba tare da yin furuci ba. Mutumin zai iya kada kansa dama da hagu (wanda hakan na alamta a’a, ba ni ba ne) ko kuma ya kada kansa sama (ma’ana eh, ni ne).

Wannan makaranta ta ‘Symbolic Interactionism’ ta ce, shi mutum yana da salo da dabarun isar da sakonni ta hanyoyi da yawa. Ta hanyar idonsa, motsi da gabobin jikinsa ko muryarsa (ba tare da yin furuci ba). Yare (language) kawai da mutum ke yi wani babban abu ne da ya nuna kololuwar darajarsa fiye da dabba. Wanda shi ma koyo ake yi ta hanyar mu’amala.

Makarantar ta ‘Symbolic Interactionism’ ta tafi kan cewa, an yi wa mutum baiwa ta iya fahimtar motsi ko wani aiki da wasu suka aikata. Mutum yana koyon abubuwa da yawa a yayin da yake mu’amala musamman da mutanen da yake ganin sune abin koyi a wurinsa. Za ka ga yana kwaikwayon salon maganarsu, salon shigarsu, salon tafiya da dai sauransu.

Sulaiman Bala Idris
+ postsBio
  • Sulaiman Bala Idris
    https://hausa.leadership.ng/author/sulaiman-bala-idris/
    Gwamna Dauda Lawal A Shekara 61:Shugaban Da Ke Gudanar Da Mulki Bisa Kyakkyawar Manufa
  • Sulaiman Bala Idris
    https://hausa.leadership.ng/author/sulaiman-bala-idris/
    Hayaniya ‘Yar Facebook!
  • Sulaiman Bala Idris
    https://hausa.leadership.ng/author/sulaiman-bala-idris/
    Mummunan Zato
  • Sulaiman Bala Idris
    https://hausa.leadership.ng/author/sulaiman-bala-idris/
    Me Ake Nufi Da Ado? 

MASU ALAKA

Zanga-Zanga: Gwamnatin Yobe Ta Bayar Da Umarnin Rufe Makarantun Jihar
Bakon Marubuci

Buni Ya Nuna Kwarewarsa Ta Diflomasiyya

August 28, 2026
An Kusa Ceto Ɗaliban Neja Da Aka Sace – Ribadu
Bakon Marubuci

Shin Tinubu Ya Tabbatar Da Sauke Ribadu Daga Mukaminsa?

August 28, 2026
Kwairanga Ya Kafa Tarihi A Shugabancin Hukumar Kula Da Kasuwar Hannun Jari Ta Nijeriya
Bakon Marubuci

Kwairanga Ya Kafa Tarihi A Shugabancin Hukumar Kula Da Kasuwar Hannun Jari Ta Nijeriya

July 24, 2026
Next Post
Bukatar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW

Bukatar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.