Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta damke wasu matasa biyu – mace da namiji bisa zargin yin aure a asirce ba tare da sani ko amincewar iyayensu ba.
Mataimakin babban kwamandan hukumar Hisbah, Sheikh Mujahidden Aminudeen ne ya tabbatar da kamen wanda ya bayyana auren a matsayin wanda ya sabawa addinin musulunci kuma ba za a yarda da shi ba.
- Gasar Zakarun Turai: Wa Aka Kora Wa Ya Wuce Zagaye Na 16?
- Ko Ina Cikin Gwamnatin Tinubu, Zan Faɗa Wa APC Gaskiya – El-Rufai
A cewar Aminuddeen, ma’auratan da aka sakaya sunansu, rahotanni sun bayyana cewa an daura aurensu ne a wani wurin shakatawa bayan wanda ya jagoranci daurin auren ya biya sadakin amaryar a daren Laraba.
Hukumar Hisbah dake da alhakin tabbatar da bin dokokin addinin musulunci da dabi’u a jihar, ta sha alwashin ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.
Aminuddeen ya nanata cewa aure abu ne mai tsarki a addinin musulunci, don haka, hukumar ba za ta lamunci duk wani wulakanci ga addinin ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp