Dan majalisar Jihar Kaduna mai wakiltar Sabon Gari, Honarabul Ali Baba ya bai wa dalibai guda 300 tallafin karatun kwamfuta, wadanda aka yaye a cikin wannan mako.
Taron yaye daliban ya gudana ne a cibiyar gudanar da taruka da ke kan titin Sokoto Road a Sabon Garin Zariya na Jihar Kaduna. An dai gabatar da daliban su 300 a gaban manyan baki don su shaida da kokarin dan majalisar.
Honorabul Ali Baba ya nuna gogiyarsa ga Allah bisa nasarar da ya samu a wannan rana. Ya kuma ya yi godiya ga dukkan malamai da sarakuna da suka sami halattar wanan taron yaye daliban da ya dauki nauyin koya masu ilimin kwamfuta, kuma ya ce hakan somin tabi ne ga jama’arsa da ikon Allah.
Dan majalisar ya bayyana ire-iren kalubalen da ya fuskanta tun farkon hawansa kujerar dan majalisa. Ya ce akawai shara’o’i da ya fuskanta da dama a lokutan baya, amma cikin ikon Allah ya sami nasara a kansu, wanda su ne sukai ta kawo masa tarnaki a kan aikin ci gaban da ke cikin zuciyarsa.
Ya sha alwashin ci gaba da bayar da kulawa ta bangaren ilmi sosai da ikon Allah.
Ya yi kira ga daliban da su yi kokari a bangaren da suka sami horon wajen amfanar da al’ummarsu.