Hon. Kwamoti Ya Kaddamar Da Cibiyar Sadarwar Zamani A Mazabarsa Da Ke Adamawa

Daga Muh’d Shafi’u Saleh, Yola

Dan majalisar wakilai mai wakiltar kananan hukumomin Numan, Demsa da Lamurde a majalisar wakilai ta kasa Kwamoti B La’ori, ya bude aiki da cibiyar na’ura mai kwakwalwa, Information and Communication Technology Center (ITC), a garin Lamurde.

Cibiyar wacce itace ta 5 daga cikin jerin ayyukan da dan majalisar ya kaddamar a bukin cika shekaru 2 da yayi kan kujerar dan majalisar wakilai mai yankin an yiwa cibiyar lakabi da marigayi Pascal Bafyau.

Da yake yiwa jama’a jawabi a taron Kwamoti La’ori, yace aikin yana daga cikin alkawuran da ya yiwa jama’ar yankin, lokacin da ya cika shekara guda.

Yace “Dama na ce zanyi, yau ga ginini agabanku na cika muku alkawarin da na dauka, na godewa Allah akan haka, na gode da irin goyon bayan da kuke nuna mini

“Yanzu Kuma wannann ba nawa bane, naku ne, dole ku kula dashi, idan mun kula dashi yaranmu zasu ci gaba da amfana da shekaru aru-aru” inji La’ori.

Da shima ke jawabi shugaban karamar hukumar Lamurde Honarable Pwadyanga William Burto, ya ce yankin bai taba samun ci gaba haka ba.

Ya ce “sai yaranmu sun tafi Mubi ko Yola kafin su yi rigistan JAM, amma yanzu a gida za su yi, muna maka godiya, Kuma nayi alkawarin zan kadange wurin” inji Burto.

Haka itama shugabar makarantar GDSS Lamurde da Mr Eric Khobe, ya wakilta ya yabawa Dan majalisar da samar da ITC a yankin.

Ya ce “Yan siyasa sukanyi alkawari 10 amma basu cikawa, Kai mamba naka alkawarin ya fita daban daga na Yan siyasa.

“Kayi mana abinda ya fidda damu daga wahalar da muke ciki lokacin rigistan ITC, mun gode da taimakon da ka mana a makarantar shekarar da ta gabata” inji Eric.

Tun da farko da yake jawabi shugaban jam’iyyar PDP na karamar hukumar Lamurde Dumas Bello, bamu tsammaci samun ITC ba, domin ITC sai a Abuja, gashi yanzu a Lamurde, mamba ya samar mana.

“Dama ance PDP bamuyi komai ba, yanzu mun samu abinda zamu nuna jama’a su gani,  da sai mun tafi Yola ko Mubi kafin mu samu ITC yanzu gashi mun samu a gida.

“Gwamna Umaru Fintiri da mamba sunyi kokari, mun gode, Muna fatan Allah ya daga darajarka ya kara daukaka, mun gode” inji Bello.

Wasu daga mahalarta taron sun hada da  Hon. Innocent Koto shugaban karamar hukumar Numan, Mista Bulus Daniel, shugaban ofishin yankin ci gaba na Gyawana, wakilan masarautar gargajiyar Bachama, kansilolin karamar hukumar Lamurde, shugabanin jam’iyyar PDP, kungiyar dattawan Lamurde, NCWS Lamurde, matasa da dai sauransu.

Haka Kuma kwararru daga hukumar National Information Technology Debelopment Agency (NITDA)  bisa jagorancin Christiana Simon, suna daga mahalarta taron bude aiki da cibiyar ICT Lamurde.

Exit mobile version