Babban jami’in gudanarwa na yankin musamman na Hong Kong (HKSAR) na kasar Sin, tare da manyan jami’an gwamnatin HKSAR da ma’aikatan gwamnati, sun halarci wani taron tunawa a hedikwatar gwamnati a yau Asabar, inda suka yi jimanin wadanda gobarar ginin gidaje ta shafa a Tai Po na Hong Kong.
An fara taron tunawa da mutanen da gobarar ta shafa ne da misalin karfe 8:00 na safe, inda aka saukar da tutar kasar Sin da tutar HKSAR zuwa rabin sanda, kana dukkan jami’an da suka halarci taron sun yi shiru na mintuna uku don nuna alhini ga wadanda gobarar ta shafa.
Ofishin Hulda na Gwamnatin Jama’ar Tsakiya a yankin HKSAR, da Ofishin Kare Tsaron Kasa na Gwamnatin Jama’ar Tsakiya a HKSAR, da Ofishin Kwamishinan Ma’aikatar Harkokin Waje ta Kasar Sin a HKSAR, da kuma Rundunar Soja ta ’Yantar da Jama’ar Kasar Sin da ke Hong Kong, sun yi shiru na dan wani lokaci da kuma saukar da tutoci zuwa rabin sanda da safiyar yau Asabar.
A cewar gwamnatin HKSAR, za a saukar da tutocin kasa da tutocin HKSAR da ke dukkan gine-ginen gwamnati da wurare daban-daban tun daga yau Asabar har zuwa Litinin.
Kazalika, za a soke ko daga duk wani biki ko taro na nishadi da gwamnati ta shirya ko ta ba da kudin shiryawa kamar yadda ya dace. (Abdulrazaq Yahuza Jere)














