Hukumar aikin Hajji ta kasa ta kara jaddada kudurinta a kan samun nasarar aikin Hajji na shekarar 2023 da ya shafi tashin maniyata zuwa kasar Saudiyya ba tare da an fuskanci wata matsala ba.
Hukumar ta bada tabbacin hakan ne ranar Litinin da yamma lokacin da take mai da martani akan wani rahoton aikin Hajjin wannan shekara mai bayanin cewar kowane maniyyaci zai biya karin dala 100.
Bayanin da mataimnakin darektan labarai da wallafe wallafe na hukumar Alhaji Mousa Ubandawaki,ya ce hukumar ba zata kasance daga cikin wani abin da zai sa a kara sa maniyata su shiga wani halin alakakai,domin bayan biyan karin dala $250 da masu kamfanonin jiragen sama suka bukata bayan an rufe sararin samaniyar kasar Sudan da taro da kamfanonin.Hukummin kula da tashohin jiragen sama da na al’amuran Hajji na Jihohi, sai hukumar taga yafi dacewa ta yi maganin matsalarda kanta.
“Hukumar ta nemi ta nemi taimakon gwamnatin tarayya data amince ta yafe masu saura kashi 35 na kudaden da za a ba kamfanonin jiragen saman wanda za su kai dala $55.Tsarin zai zama wani karin kudi ne da zai kasance ne akan maniyyatan Nijeriya.
Tun da farko gwamnatin tarayya ta yafe masu kashi 65 na kudaden da hukumar kula da jiragen sama ga maniyyata zuwa aikin Hajji.Idan aka yi la’akari da karin dala $250 da aka yi da kamfanonin jiragen sama za a rage su da dala $55.
“Sauran dala $195 maniyyata 75,000 ne za su biya inda kowane maniyyaci zai biya dala $117.
“La’akari da aka yi biyan dala $117 na iya kasancewa karin wahala ga maniyyata, shi yasa hukumar ta yanke shawarar a rage kudin tafiyar na Hajjin 2023 daga dala 800 zuwa dala700 kamar yadda su maniyyatan suka biya dala 800.
“Maganar sauran dala $17 bugu da kari hukumar ta sake neman hadin kan kamfanonin jiragen sama su dauki al’amarin dala 17 a matsayin wata garabasa ce ga maniyyatan Nijeriya wadanda tuni al’amarin rufe sararin samaniyar Sudan ya shafe su.
“Saboda haka ne muke ta kara kira na cewa da zarar an kare takaddamar tashin hankali da ke faruwa a kasar Sudan idan aka samu damar kawo karshen ta, wanda zai sa a ci gaba da zurga- zurgar jiragen sama,hakan zai sa a sake maidawa mainiyyata wasu kudaden kamar yadda hukumar ta bayyana.
Wannan ya nuna ke nan:“Idan har ya kasance halin daake cikin Sudan ya sa ahar an rufe sararin samaniyarta saboda al’amarin daya shafi tsaro.
Irin hakan zai sa a samu wasu hanyoyin sararin samaniya da jiragen saman za su bi,ana iya samun karin awa daya da rabi ko kuma awa uku, wannan ya danganta ne daga wurin da jirgin zai tashi a Nijeriya.
Wannan sabuwar hanya ta sararin samaniya zai sa kamfanonin jiragen saman su bi ta sararin samaniyar kasashen.
Kamaru,jamhuriyyar Afirka ta tsakiya,Uganda, Kenya,Habasha da kuma Eriteriya, da karin kudin man jirgi, sai kuma karin kudin lokacin da aka yi ana tafiya.