A daren ranar litinin din nan ne za a fara fitar da jadawalin gasar cin kofin nahiyar Afirka na shekarar 2025, hukumar kula da kwallon kafa ta Afirka CAF da kuma kananan hukumomin kwallon kafa (LOC) sun bayyana garuruwan da za su karbi bakuncin wasannin a kasar Morocco.
An zabo birane shida da filayen wasa tara don gudanar da gasar kwallon kafa ta nahiyar Afirka, wadda za ta gudana daga ranar 21 ga Disamba, 2025 zuwa 18 ga Janairu, 2026.
Garuruwan sune Rabat, Casablanca, Agadir, Marrakech, Fes da Tangier.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp