Hukumar da ke kula da gidajen yari ta Nijeriya NCoS, a safiyar Laraba, ta tabbatar da harin da wasu ‘yan bindiga suka kai a Cibiyar ta da ke Unguwar Kuje a Abuja.
A wata sanarwa da mai magana da yawun NCoS, Umar Abubakar, wanda LEADERSHIP ta samu, hukumar ta ce har yanzu ba ta gano wadanda suka kai harin ba.
Sanarwar ba ta kuma bayyana ko an samu asarar rayuka ko fasa gidan yarin sakamakon harin ba.
“Ina so in tabbatar da cewa da misalin karfe 10:00 na daren Talata, wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun kai hari a cibiyar Gidan Gyara-hali da ke Kuje a babban birnin tarayya.
“Jami’an tsaron cibiyar da sauran jami’an tsaro da ke kula da tsaron cibiyar sun samu nasarar dakile harin kuma tuni al’amuran cibiyar suka koma dai-dai.
“Za mu kawo Sauran bayanai nan ba da jimawa ba,” in ji Abubakar.