Hukumar Kula da Gidajen Yari, ta tabbatar da cewa wani fursuna guda daya ya rasu a gidan yarin Kuje sakamakon fama da rashin lafiya.
Kwanturolan hukumar na birnin tarayya, Ahmed Musa Ahmed, ne ya tabbatar da mutuwar fursunan, yana mai mika jajensa da ta’aziyyar ga ahalin mamacin bisa rashin da suka yin.
- Yadda Bidiyon Tsiraicina Ya Karade Shafukan Sada Zumunta – Safara’u
- Kotu Ta Sake Hana Ba Da Belin Abba Kyari
Ya nanata aniyar hukumar na ci gaba da mayar da hankali sosai wajen kula da lafiyar fursunoni da kuma ma’aikatan gidan yari a kowane lokaci.
A wata sanarwar da kakakin hukumar na Abuja, Chukwuedo Humphrey, ya fitar, ya ce fursunan ya mutu ne bayan fama da rashin lafiya, kuma an masa jinyar wasu cututtuka yadda ya kamata.
Ahmed, ya shawarci fursunonin da suke kan amsar wasu magunanna musamman da suke fitowa su fada musu domin fuskantar cututtukan da ke damunsu a kowane lokaci tun da magunguna suna nan kuma kyauta ake basu.
Sanarwar ta kara da cewa, “Cikin gaggawa an dora mamacin kan samun kulawar magani ta musamman kafin rasuwarsa har ma sai da ta kai an sauya masa wurin jinya zuwa asibitin koyarwa a Jami’ar Abuja da ke Gwagwalada domin samun kulawar likitoci yadda ya kamata.
“Abun takaici, a lokacin da jikin mamacin ya tsananta a karshen mako, duk kokarin da likitoci suka yi domin ceto rayuwarsa abun ya ci tura kwanansa ya kare.”
Ya ce an shirya wa mamacin addu’a ta musamman a gidan yarin domin nema masa salama.
Kazalika wasu ma’aikatan gidan yari da suka zanta da LEADERSHIP sun zargi rashin kula daga hukumar kula da gidajen yarin.
Ma’aikatan da suka nemi a sakaya sunansu, sun ce kalubalen matsalar ingancin kayan kula da lafiyar fursunoni na daga cikin manyan matsalolin da suke addabar gidan yarin.
Sun kuma yi zargin cewa wanda ya mutu bai samu kulawar da ta dace ba tun lokacin da ya fara jinya.